Adamawa ta soke biyan kudin makaranta, ta farfado da shirin ciyarwa

Adamawa ta soke biyan kudin makaranta, ta farfado da shirin ciyarwa

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umar Fintiri ya sanar da koyarwa kyauta ga daliban makarantar sakandare a jihar domin inganta kokari da ba iyaye talakawa damar tura yaransu makaranta.

Fintiri yayi sanarwar ne yayinda ya karbi bakuncin mambobin jam’aiyyar African Democratic Congress (ADC) karkashin jagorancin dan takarar gwamnanta a zaben 2019, Sanata Abdul-Azeez Nyako, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa na gidan gwamnati, Yola.

Gwamnan yace manufar tsarin, wanda zai fara aiki a watan Disamba, shine domin ba yara da suka fito daga tsatson talakawa su samu damar yin karatu, inda ya bayyana cewa gwamnatinsa zata jajirce wajen inganta makarantun gwamnati domin ta yadda za su dawo kamar na kudi.

Bugu da kari, Gwamna Fintiri yace gwamnatinsa za ta farfado da shitin ciyar da daliban makarantun kwana sannan ba da jimawa ba zai karade dukkanin makarantun kwana 65 da ke jihar.

KU KARANTA KUMA: To fah: Sai saurayi ya bani naira miliyan biyu kafin nayi soyayya da shi - Jaruma Toyin Lawani

Iyaye na biyan tsakanin N1,000 da N1,500 a matsayin kudin makarantar kowani dalibi, kai tsaye ga makarantun, hukumomin marantun kan yi amfani da kudaden wajen gudanar da harkokin yau da kullun, yayinda daliban makarantun kwana ke biyan N4,500 a matsayin kudin makaranta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel