Yan bindiga sun kashe wani babban dan kasuwa, sun kuma sace matar dansa a Kebbi

Yan bindiga sun kashe wani babban dan kasuwa, sun kuma sace matar dansa a Kebbi

Rahotanni sun kawo cewa a safiyar ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli wasu yan bindiga, sun kashe wani fitaccen dan kasuwa a garin Gulma da ke jihar Kebbi, Alhaji Usuf Garkar-Bore sannan suka yi garkuwa da surukarsa, Aisha.

Wani mamba a garin, wanda ya nemi a boye snansa, yace aan kashe an kashe Alhaji Garkar-Bore mai shekara 6, da misalin karfe 2:00 na tsakar daren ranar Lahadi. Yace yan bindigan sun harbe shi sau da dama a kirji a lokacin da suka yi nasarar shiga gidansa a Gulma.

“Dan sa ya tafi fatauci lokacin da maharani suka kai mamaya gidan nasa. Sun yi nasarar shiga gidan bayan sun yanke wayar lantarki da ke kewaye da katangar gidan,” in ji shi.

An tattaro cewa an kai Alhaji Garkar-Bore babban asibitin Argungu domn samun kulawar likita amma sai aka tabbatar da mutuwarsa sannan tuni aka binne sa daidai da koyarwar musulunci.

an kuma rahoto cewa kafin su tafi da surukarsa, yan bindigan sun yi amfani da jakar makarantar daya daga cikin yaransa wajen kwasar kudade masu yawa a gidan wanda suka tafi dashi.

KU KARANTA KUMA: Daga yanzu yan sanda da sojoji na da ikon daukar kowani irin mataki kan yan shi’a – Fadar Shugaban kasa

Kakakin yan sanda a jihar, DSP Nafiu Aubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an zuba jami’an tsaro a yankin domin su kamo maharan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel