Kungiyar Shi’a ta yi watsi da El-Zakzaky, ta bayyana IMN a matsayin mai hatsari

Kungiyar Shi’a ta yi watsi da El-Zakzaky, ta bayyana IMN a matsayin mai hatsari

- Wani bangare na kungiyar Shi’a sun yi Allah wadai da ayyukan kungiyar IMN

- Kungiyar tace IMN bata wakiltan addinin Shi’a

- Babban sakataren kungiyar, Sheikh Hamza Muhammad Lawal, yayi kira ga Gwamna El-Rufai da ya janye shari’arsa akan kungiyar

Gidauniyar Al-Thaqalayn wacce ta kasance bangare guda na kungiyar Shi’a ta bayyana kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) wacca Sheikh Ibraheem El-Zakzaky ke jagoranta a matsayin na jabu.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Sheikh Hamza Muhammad Lawal wanda ya kasance babban sakataren kungiyar ya bayyana hakan a ranar Talata, 30 ga watan Yuli a Kaduna.

Yayi bayanin cewa addinin Shi’a bai yi daidai da IMN ba sannan cewa kada a dunga musayar kungiyoyin biyu.

Lawal ya bayyana bangaren da El-Zakzaky ke jagoranta a matsayin mai hatsari da rashin alkibla inda ya bayyana ta a matsayin na jabu.

Lawal yace ya taba kasancewa mamba a kungiyar IMN tsakanin 1981 da 2000, shekara guda bayan ya dawo daga Qum, Jumhuriyyar Musulunci na Iran, inda ya karanci bangaren ilimin tauhidi.

KU KARANTA KUMA: An gama da ainahin Boko Haram, in ji Fadar shugaban kasa

Malamin addinin yace a dunga kiran bangaren El-Zakzaky da IMN wanda ita ta zaba a matsayin sunanta amma ba wai Shi’a ba domin ba daya suke ba.

Malamin yayi kira ga Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna da ya janye shari’ansa akan El-Zakzaky sanan ya kuma bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari “ya sasanta da mambobin IMN.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel