Karin bayani: Babu abunda ya samu dana yana nan da ransa – Tijjani Asase (bidiyo)

Karin bayani: Babu abunda ya samu dana yana nan da ransa – Tijjani Asase (bidiyo)

Fitaccen jarumn Kannywood mai suna Tijjani Asase ya karyata rade-radin da ke yawo kan cewa barayin Babura sun kashe dansa mai suna Sadauki.

Yace suna nan lafiya daga ciki har dansa, babu wani matsala daya faru dashi.

Sannan ya mika godiya ga abokan sana’arsa da suka daga hankalinsu bayan samun labarin cewa ibtila’i ya afka ma iyalinsa.

Da safiyar yau ne dai aka tashi da labarin cewa Allah ya yi wa yaron jarumin rasuwa, bayan barayin babura sun far masa a Unguwar Gaida da ke Kano.

Sai dai kuma jarumin yawallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram inda ya karyata lamarin n yace; "Salam barkanmu da wannan lokaci ina mika godiyata Allah da yabani ikon karyata zance da yake yawo wai namutu wai ankashe dana sadauki Dan haka nake sanarda karyata hakan,nagode wa abokan sana'ata da masoya Dasuka nuna damuwarsu akaina."

Ga bidiyon a kasa:

KU KARANTA KUMA: Mansurah Isah ta nemi Hadiza Gabon da Maryam Yahaya su yi karan Tanimu Akawu kan kalaman cewa matan Fim suna bin mazan banza

A wani labari na daban, Legit.ng ta rahoto a baya cewa a ranar Asabar ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kashe masu zaman makoki 23 yayin da suke dawowa daga binne wata gawa a jihar Borno.

A cewar Bunu Bukar Mustapha, shugaban kungiyar 'Yansakai, mayakan dake kan babura guda uku sun kai wa tawagar masu raka gawar hari a yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga makabarta bayan binne gawar mamacin a yankin Nganzai da ke daf da Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel