Abunda zai faru da jikin mutum idan yana da ciwon Hanta

Abunda zai faru da jikin mutum idan yana da ciwon Hanta

Idan aka ce Hepatitis, toh ana nufin ciwon Hanta kenan a Hausance. Hepatitis kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, Hepatitis B, Hepatitis C, Hepatitis D, Hepatitis E.

Cikinsu akwai masu acewa da kansu bayan sun kama mutum, wasunsu kuma sai an hada da magani. Hakazalika wasunsu ba sa tsananta, wasu kuma suna tsananta.

Sai dai kuma bincike ya nuna cewa Hepatitis A, Hepatitis B, da Kuma Hepatitis C su ne suka fi Wanzuwa tsakanin mutane.

Alamomin ciwon hanta:

1. Ciwon Ciki

2. Zafin Jiki

3. Amai

4. Tashin Zuciya

5. Kasala

6. Bakin Fitsari

7. Idanuwa su yi kalar dorawa da jiki

8. Kaikayin jiki

9. Bahaya kore

Zaka iya samun gkarin bayani akan cutar Hepatitis A,B,C,D,E a kasa:

Hepatitis A

Kwayar cuta mai suna Hepatitis A Virus ce ke haddasa shi.

Ana kamuwa dashi ne ta hanyar gurbatuwar abinci ko ruwan sha wanda ya gaurayu da kashin wani mai dauke da cutar, wanda kwari ke yadawa, sannan ya fi yaduwa ne a kasashen da tsaftar muhalli ke da karanci.

Hepatitis B

Kwayar cutar hepatitis B virus ce ke haddasa wannan rukuni na ciwon hanta, wanda ke yaduwa a cikin jinin mutumin da ya kamu da ita.

Ana kamuwa dashi ne idan aka sanya wa mutum jinin mutumin da ke dauke da ita, yin amfani da allura ko reza, ko wasu karafa masu dauke da kwayar cutar. Hakazalika ana dauka daga Uwa zuwa danta, da kuma saduwa da wanda ke dauke da cutar.

Hepatitis C

Ana kamuwa dashine ta kwayar cutar Hepatitis C . Yana yaduwa ne ta hanyar sanya wa mutum jinin wanda ke dauke da ita.

Hepatitis D

Ana kamuwa dashi ne ta kwayar cutar Hepatitis D. Yana shafar mutumin da ya riga ya kamu da cutar hepatitis B ne, domin yanabukatar kwayar cutar hepatitis B kafin ya iya tsira a jikin mutun.

Yan yaduwa ta hanyar sanya wa mutum jinin mai dauke da ita da kuma saduwa da wanda ke dauke da cutar.

Dadewar wannan cuta na iya sa mutum kamuwa da cutar dajin hanta.

Hepatitis E

Ana kamuwa dashi ne ta kwayar cutar hepatitis E. Sannan akan kamu dashi ne ta hanyar cin danyen naman alade.

Wannan baya dadewa a jikin mutum, sannan baya bukatar kowani magani, amma ya kan munana a cikin wasu mutane.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng