Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa mahaifin gwamnan Adamawa rasuwa

Yanzu Yanzu: Allah ya yi wa mahaifin gwamnan Adamawa rasuwa

Alhaji Umaru Badami, mahaifin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa, ya rasu.

Badami mai shekara 82, ya rasu ne a ranar Lahadi, 28 ga watan Yuli, bayan yayi fama da rashin lafiya, Solomon Kumangar, darakta janar na labaran gwamnan ya fada ma kafanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Yola.

Ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne da misalin karfe 2:30 na rana.

“Ya kwanta jinya a asibitin tarayya, Yola sannan an sallame shi a jiya kawai sai ya yanke jiki ya fadi daga bisani,” Kumagar ya sanar da NAN.

Marigayin wanda ya kasance soja mai ritaya, ya rasu ya bar matar aure daya da yara shida, ciki harda Gwamna Fintiri.

NAN ta ruwaito cewa an binne Badami daidai da koyarwar addinin Musulunci bayan an yi masa sallar jana’iza a babban masallacin Juma’a na Yola.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari ta yi kira ga jama’a da su kokarin kallon fim din Hausa mai suna Hauwa Kulu

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto cewa Fitaccen jarumin Kannywood mai suna Tijjani Asase ya karyata rade-radin da ke yawo kan cewa barayin Babura sun kashe dansa mai suna Sadauki.

Yace suna nan lafiya daga ciki har dansa, babu wani matsala daya faru dashi. Sannan ya mika godiya ga abokan sana’arsa da suka daga hankalinsu bayan samun labarin cewa ibtila’i ya afka ma iyalinsa.

Da safiyar yau ne dai aka tashi da labarin cewa Allah ya yi wa yaron jarumin rasuwa, bayan barayin babura sun far masa a Unguwar Gaida da ke Kano.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel