Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Daga cikin kokarin da ya ke yi na bayar da tallafi ga jama’a a kudancin jihar Borno, Gwamna Babagana Umara Zulum ya ziyarci Damboa a ranar Juma’a, 3 ga watan Janairu domin rabon kayan abinci da sauran kayayyakin amfani.
Rahotanni sun kawo cewa an cafke wani mutum da ake zargi da hadawa tare da yada bidiyon aure na bogi tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministarsa.
Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da mutane biyar a karamar hukumar Gassol da ke jihar Taraba. Lamarin a cewar idon shaida ya faru a tsakanin Sabongida zuwa WuroJam a karamar hukumar Gassol da ke jihar Taraba a ranar Laraba.
Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kashe akalla mutane 19 a garin Tawari a dake karamar hukumar Kogi, jihar Kogi inda suka kona wasu gine-gine ciki harda faar sarkin garin.
Rundunar sojin sama na Najeriya ta lalata wani ginin ajiye kayayyakin jin dadi na yan ta’addan Boko Haram a Gujeri da ke dajin Sambisa a jihar Borno. Rundunar ta ce an aiwatar da aikin ne ta jirgin yakin Operation Lafiya Dole.
Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole ya bayyana cewa masu neman ya yi murabus hassada da bakin ciki suke yi masa, ganin cewa ya taka rawar ganin da ba a taba takawa ba a jam’iyyar.
Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Godfrey Dikeocha ya yaba ma kudirin yaki da rashawar shugaban kasa Muhammadu Buhari yayinda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa kasar Amurka ta kashe babban kwamandan dakarun sojojin juyin-juya hali na kasar Iran, Qasem Soleimani a wani harin sama da sojojinta suka kai filin jirgin sama na Bagadaza, a kasar Iraki.
Rahotanni sun kawo cewa wasu malaman makarantun Firamare na jihar Kano sun koka kan cewa har yanzu ikirarin da gwamnatin jihar ke yin a cewar ta fara aiwatar da sabon karancin albashi na 30,000 bai iso wajensu ba.
Aisha Musa
Samu kari