An harbe jami’an yan sanda 2 a wani harin bazata da Boko Haram ta kai

An harbe jami’an yan sanda 2 a wani harin bazata da Boko Haram ta kai

Rahotanni sun kawo cewa akalla jami’an yan sanda biyu ne suka rasa ransu a ranar Litinin bayan an harbe su a wani harin bazata da yan ta’addan Boko Haram suka kai a jihar Yobe.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa harin ya afku ne a babban titin Maiduguri-Damaturu.

Kwamishinan yan sandan jihar Borno, Mohammed Aliyu ya tabbatar da harin amma ya ce babu jami’in da ya mutu.

Amma kuka wani idon shaida ya ce ya ga jami’an yan sanda biyu kwance a kasa a safiyar ranar Litinin yayinda rundunar tsarosuka umurci dukkanin matafiya zuwa Damaturu, babbar birnin jihar Yobe, da su koma Maiduguri.

“Ina ganin babu mamaki sun mutu ne sakamakon harin,” inji wani direban motar kasuwa da ya bayyana sunansa a matsayin Bukar Modu.

A cewarsa lamarin ya afku ne a tsakanin Jakana da Mainok. A yanzu garuruwan biyu na fama da karin hare-hare daga Boko Haram.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda 103 aka kashe a shekarar 2019 - Lissafi

An tattaro cewa an mayar da dakarun sojin Bogozo zuwa Jakana duk daga cikin matakan tsare matafiya a hanyar babban titin Damaturu/Maiduguri.

Wani direba ya bayyana cewa motocin da ke fitowa daga Damaturu kadai ne ake bari su shiga Maiduguri yayinda aka hana masu fitowa daga Maiduguri wucewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel