Davido: Malamin Musulunci Ya Yi wa Rarara Wankin Babban Bargo kan Tsaro
- Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya caccaki mawaki Dauda Kahutu Rarara, yana zarginsa da rashin kishin Arewa
- Malamin ya nuna fushi kan kalaman da Rarara ya yi game da malamai, yana mai cewa ya daɗe yana wa’azi tun kafin mawakin ya shahara
- Sheikh Alkali ya gargadi Rarara ka da ya soki Bola Tinubu bayan mulkinsa, yana tunatar da shi yadda suka yi addu’o’i lokacin da aka sace mahaifiyarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya yi magana game da abin da ke faruwa a Arewa.
Malamin ya caccaki Dauda Kahutu Rarara game da rigimar da ta balle tsakaninsa da mawaki a Kudancin Najeriya, Davido.

Source: Facebook
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da shafin Abdullahin Gwandu TV ya wallafa a Facebook a jiya Alhamis 18 ga watan Yunin 2026.
Malami ya caccaki Rarara kan rashin kishi
Malamin ya dura kan Rarara inda ya ce kwata-kwata matashin ba shi da kishin yankinsa duba da abubuwan da suke faruwa.
Sheikh Alkali Zaria ya kuma nuna fushina game da yadda Rarara ya kira wasu malamai da cewa sun bar karatu sun koma neman mabiya.
Ya ce:
"Za ka ci uwaka Rarara, bari su gama dole da mu zaka zauna, mu ne wadanda za mu fada maka gaskiya.
"Waye bai sanka ba, dazu na ga yana cewa wai malamai sun dena karatun Allah sun koma karatun neman mabiya.
"Mu za ka duba ka ce muna karatun neman mabiya, wallahi tun kafin a san ka, ni aka san ni, wannan kujerar da ku ke ganin tun 1995 na ke wa'azi."

Source: Facebook
Yadda Rarara ya caccaki Buhari a baya
Malamin ya tuna irin bakaken maganganu da Rarara ya fada wa marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Ya yi masa gargadi da cewa ka da ya kuskura Bola Tinubu ya gama mulkinsa ya zo ya ce zai fada wa mutane illarsa.
"Wace magana ce bai fada wa Buhari ba, karya ka ke Tinubu ya sauka ka ce zaka fada mana illarsa, sai na faffasa maka baki.
"Babu wanda zai mana iskanci a Arewa mu zuba masa ido wallahi, mahaifiyarka aka sace, nan muka rika rokon Allah har aka dawo da ita.
"Me kake nema wanda Allah bai baka ba, kudin nan ka samu, daukakar nan Allah ya daukaka ka, wakar nan ka iya, tun ana ji har an daina sauraronka."
- Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria
Shehi ya yi addu'a ga azzaluman shugabanni
Mun ba ku labarin cewa wani bidiyo ya bayyana lokacin da Sheikh Alkali Abubakar Salihu Zaria ya yi addu’ar fatan mutuwar shugabannin da ba su da cancanta.
Malamin ya yi addu'o'in ne a gaban dan takarar shugaban kasa a 2023, Peter Obi yayin ziyararsa a Kaduna.
Sheikh ya yi addu'ar duk wanda ba zai zama alheri ba ga Najeriya idan ya ci zabe, Allah ya karɓi ransa kafin zabe.
Asali: Legit.ng

