Tsohon kakakin majalisar dokokin Imo ya sauya sheka zuwa APC

Tsohon kakakin majalisar dokokin Imo ya sauya sheka zuwa APC

Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Imo, Godfrey Dikeocha ya yaba ma kudirin yaki da rashawar shugaban kasa Muhammadu Buhari yayinda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Dikeocha, wanda ya kasance tsohon jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya jinjina wa yaki da rashawarar da Shugaban kasar ke yi ne a gidansa da ke Ndigbo Uvuru, karamar hukumar Aboh Mbaise lokacin da shugabannin APC suka ziyarce shi.

Tsohon kakakin majalisar ya ce manufar yaki da rashawar Buhari ya kawo ci gaba sosai a kasar.

Ya ce: “Na yarda da tsarin yaki da rashawar Shugaban kasa, kuma yana yakar lamarin duk da kalubalen da ke tattare dashi. Duk da rashin samun goyon baya daga kudu maso gabas, Shugaban kasar na yiwa yankin ayyuka masu muhimmanci.

“Ko a zamanin PDP, Mun gaza aikin gadar 2nd Niger amma a yau gashi ana gudanar da aikin wajen, ciki harda aikin gyare-garen filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke gudana.

“Mutanen kudu maso gabas wandanda yan PDP ne sun riki mukaman ministoci sannan ba su yi komai don bunkasa filin jirgin ba, amma Shugaban kasar na aiki na gani na fada duk da rashin samun kuri’u daga yankin.”

Dikeocha ya kuma bukaci Shugaban kasar da ya isar da aikin tashar jirgin kasa har zuwa kudu maso gabas.

KU KARANTA KUMA: Amurka ta kashe babban kwamandan sojin Iran

Jigon jam’iyyar ya sha alwashin taimakawa wajen sake gina APC a jihar, cewa lokaci ya yi da yan Igbo za su hada hannu don cigaban kasar.

Ya kuma bukaci Sanata Rochas Okorocha, Uche Nwosu, da Hope Uzodinma da su hada kai don cimma nasara a gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel