Gwamnonin arewa sun gargadi gwamnatin tarayya kan janye dakarun soji

Gwamnonin arewa sun gargadi gwamnatin tarayya kan janye dakarun soji

Kungiyar gwamnonin arewa a karshen makon da ya gabata sun bukaci gwamnatin tarayya da ta yi hankali a shirinta na janye dakarun sojoji daga yankuna marasa tabbass.

Gwamnatin tarayya a ranar Litinin da ya gabata bayan wata ganawa da majalisar tsaro ta kasa karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa daga kwatan farko na wannan shekarar, za ta fara janye ayyukan sojoji a wasu yankunan kasar.

Shugaba hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas, wanda ya yi jawabi ga manema labarai bayan ganawar, ya jadadda cewa za a janye dakarun ne bayan anyi tankade da rairaya domin sanin yankunan da zaman lafiya ya dawo domin ba hukumomin tsaro na yan sanda cikakkiyar damar jan ragawar tsaro a wajen.

Har ila yau a ranar Juma’a, Shugaba Buhari ya sake bayar da tabbacin cewa ba za a janye sojojin daga yankunan da zaman lafiya ya dawo ba ta yadda za a iya kaiwa garuruwan hari ba.

Shugaban kasar ya bayar da tabbacin cewa a hankali za a janye su sannan kuma a tsanaki za a yi hakan don kada a tarwatsa nasarar a sojojin suka riga suka samu.

KU KARANTA KUMA: An kashe kyaftin din rundunar sojin Najeriya da wasu dakarun soji 3 a kauyen Neja

Amma Shugaban kungiyar gwamnonin arewan kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, a wata hira da jaridar Daily Trust, ya bayar da shawarar cewa a yi hankali wajen janye dakarun, musamman daga jihohi marasa tabbass ina gwamnoni da masu ruwa da tsaki suka fara sanya karfin gwiwa a zukatan mutane.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel