Gwamnatin tarayya ta bayyana jakadun da aka tsige

Gwamnatin tarayya ta bayyana jakadun da aka tsige

Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari,ta yi watsi da rahotannin cewa ta yiwa jakadun kasar da dama kiranye.

Rahotannin kafofin watsa labarai sun yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta tsige jakadunta da dama a kashashen waje.

Amma Mallam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wani jawabi da ya saki ya ce jakadu 25 wadanda suka cika shekarun ritaya ko shekaru 35 na ka’idar aikin gwamnati kadai aka yiwa kiranye.

“Babu wani abu mai kama da tsige jakadu da yawa. Abunda ya faru shine an sallami jakadu 25 ne wadanda suka cika shekarun ritaya ko shekaru 35 na ka’idar aikin gwamnati a Disamba 2018.

“An bar su sun ci gaba da aikinsu bayan an tsawaita wa’adinsu, domin zabukan da suka gabato wanda a yanzu suka wuce,

“Baya ga wadannan babu wani jakada da aka tsige”, inji sanarwar.

KU KARANTA KUMA: Fasto Bakare ya bayyana ainahin makiyan Najeriya

A baya mun ji cewa Gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da janye jakadu da shugabannin hukumomin waje su guda 25.

Tabbatarwar ya biyo bayan turjiya da aka samu daga jakadun da lamarin ya shafa wadanda suka ce wa’adin Disamba 31, 2019 da aka basu ya yi kusa da yawa.

Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama, ya aika wa jakadun rubutacciyar wasika a watan Nuwamba, inda ya yi umurnin cewa su dawo Najeriya a ranar ko kafin 31 ga watan Disamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel