An kashe kyaftin din rundunar sojin Najeriya da wasu dakarun soji 3 a kauyen Neja

An kashe kyaftin din rundunar sojin Najeriya da wasu dakarun soji 3 a kauyen Neja

Wasu yan bindiga sun kashe wani kyaftin din rundunar sojin Najeriya da dakarun sojoji uku a wani harin bazata da suka kai Sarkin Pawa a karamar hukumar Munya da ke jihar Neja.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa sojoji uku sun ji rauni a harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar Kyaftin din da ya jagoranci sojojin – wani sajan, da kofur biyu a wani aiki da suka yi a yankin.

An tattaro cewa sojojin da suka mutu sun amsa kiran neman dauki da mutanen garin Gwar da ke karamar hukumar Munya suka yi masu ne lokacin a lamarin ya afku.

Yan bindigan sun kai mamaya yankin inda suke shiga gidaje daya bayan daya amma ba tare da bata lokaci ba tawagar tsaro da aka kai yankin daga sansanin garin Zazzaga suka far masu.

Sai yan bindigan suka tsere jeji inda suka kaiwa tawagar wadanda suka samu rakiyar wasu jami’an yan sanda harin bazata a motar yakinsu.

Da suka hangi tawagar, sai yan bindigan suka bude masu wuta inda suka kashe kyaftin din a nan take yayinda suka samu sojojin a lokacin da suke musayar wuta wanda ya shafe tsawon sa’a guda.

Hakazalika, an kona motocin Hilux guda biyu yayinda yan bindigan suka tsere da bindigar tawagar.

KU KARANTA KUMA: Shugabancin kasa: Har yanzu arewa na da sauran wa’adi daya - Owie

Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban karamar hukumar Munya, Mohammed Dazz, ya ce yan bindigan kimanin su 30 ne suka kai farmaki garin.

Ya kuma bayyana cewa an kai gawawwakin sojojin zuwa ofishin yan sanan Sarkin Pawa bayan faruwar lamarin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel