Bayan Iran, Isra'ila Ta Fara Barazanar kai Hari Wata Kasar Musulunci
- Ministan Benjamin Netanyahu, Amichai Chikli ya yi barazanar cewa Isra’ila za ta iya kai wa Siriya hari a wani lokaci mai zuwa komai dadewa
- Chikli ya zargi wasu kasashe kamar Qatar,Turkiyya da Pakistan da taka rawa wajen tsara yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran
- Kalaman ministan sun zo ne bayan rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin Amurka da Iran domin kawo ƙarshen yaƙin da suka yi a Gabas ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Isra'ila - Ministan harkokin wajen Isra’ila, Amichai Chikli, ya yi barazanar cewa Isra’ila za ta yaƙi Siriya ko ba dade ko ba jima.
A wani taro da ya yi magana, Chikli ya yi ikirarin cewa kasashen Siriya da Turkiyya sun fi Iran zama barazana ga Isra’ila a halin yanzu.

Source: Getty Images
Isra'ila za ta kai hari Siriya
Rahoton Anadolu Agency ya nuna cewa Chikli ya ce suna ganin cewa Siriya ta zama masu barazana a Gabas ta Tsakiya.
“Za mu yaƙi Siriya, ko ba dade ko ba jima, domin ita da Turkiyya sun fi Iran tayar mana da hankali,” in ji Chikli a wata hira da gidan rediyon Isra’ila na 103FM.
Kalaman Chikli, wanda mamba ne a jam’iyyar Likud mai mulki ta Firaminista Benjamin Netanyahu, sun zo ne sa’o’i kaɗan bayan Iran da Amurka sun rattaba hannu kan wata takardar fahimtar juna da ke da nufin kawo ƙarshen yaƙi a dukkanin fagage.
Ministan Isra’ila ya sha yin suka ga ƙasashen yankin da ke taka rawa a ƙoƙarin diflomasiyya na kawo ƙarshen rikice-rikicen da ake fama da su.
Isra'ila ta soki kasashe 3
A ranar Laraba, Chikli ya nuna adawarsa ga abin da ya kira “ƙawancen Qatar da Turkiyya da Pakistan,” yana zargin ƙasashen uku da taka rawa wajen tsara yarjejeniyar da ke tsakanin Washington da Tehran.
“Yarjejeniyar da ake shirin kammalawa ta tayar da hankali, amma abin da ya fi damuna ba shi ne farfaɗowar tattalin arzikin Iran ba,”
In ji shi, yana nuni da barnar da yaƙi da shekaru na takunkumi suka haifar.

Source: Getty Images
TRT ta wallafa cewa Chikli ya ce babban abin da ke damunsa shi ne abin da ya bayyana a matsayin ƙawancen da ya tsara wannan yarjejeniya: Qatar, Turkiyya da Pakistan.
“Abin da muke gani a gabanmu shi ne bullowar wani sabon ƙawance,”
In ji shi yayin da ya ke sukar kasashen Gabas ta Tsakiya.
Amurka ta gargadi Isra'ila
A wani labarin, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya gargadi jami'an gwamnatin Benjamin Netanyahu.
Vance ya ce wasu daga cikin shugabannin Isra'ila na sukar Donald Trump kan yarjejeniyar da ya kulla da Iran, wanda hakan bai dace ba.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa Amurka ce kadai ta ragewa Isra'ila a halin yanzu, inda ya ce dukkan kasashen duniya sun juyawa Tel Aviv baya.
Asali: Legit.ng

