Da Gaske Yan Ta’adda Sun Harbo Jirgin Sojojin Sama a Niger? Bayanai Sun Fito
- Mutane da dama sun yi ta yada wani bidiyo cewa yan bindiga sun harbo wani jirgin saman Najeriya a jihar Niger
- Bincike ya gano babu wata hujja da ke tabbatar da ikirarin cewa ‘yan ta’adda sun harbo jirgin saman rundunar sojoji kamar yadda ake fada
- Masu binciken sun gano bidiyon da aka yada tsohon faifai ne daga hatsarin jirgin saman da ya faru a Shiroro a shekarar 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zungeru, Niger - Wasu masu amfani da kafofin sadarwa sun tayar da hankalin al'umma game da bidiyon harbo jirgin saman Najeriya.
Hakan ya jawo maganganu wanda a tayar da hankulan yan Najeriya da suke ganin lallai akwai babbar matsala kan matsalar tsaro.

Source: Twitter
Bidiyon da ake yadawa a kafofin sadarwa
Wani mai amfani da shafin X mai suna @Comrdebarde ya wallafa bidiyon yana ikirarin cewa ‘yan ta’adda sun harbo jirgin rundunar sojin saman Najeriya a Zungeru da bindigar AK-47.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto mutanen da aka gani a bidiyo tare da Janar Rabe a hannun 'yan bindiga
Mutumin ya kuma yi iƙirarin cewa lamarin ya faru kwanan nan, bayan wani mai amfani da shafin ya tambaye shi ko bidiyon da aka nuna sabon abu ne.
Bidiyon ya nuna wani jirgin sama da ya lalace tare da gawarwaki a kusa da shi, yayin da wasu dauke da makamai ke zagayawa suna yin kabbara.
Gaskiyar lamari kan jita-jitar da ake yadawa
Saboda tasirin da irin wannan ikirari zai iya yi ga fahimtar jama’a game da tsaro, cibiyar binciken gaskiya ta shafin Dubawa ya gudanar da bincike kan lamarin.
Masu binciken sun yi amfani da kayan aikin InVID domin fitar da hotuna daga bidiyon tare da gudanar da binciken gano asalin hotunan ta hanyar intanet.
Sakamakon binciken ya kai su ga wani rahoto da aka wallafa a watan Agustan 2023 game da hatsarin jirgin NAF MI-171E da ya faɗi a ƙauyen Chukuba na ƙaramar hukumar Shiroro.
Rahotannin jaridun The Cable da Punch sun kuma tabbatar da hatsarin jirgin da ya auku a ranar 14 ga Agustan 2023 a Niger.
Mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya a lokacin, Air Commodore Edward Gabkwet, ya tabbatar da aukuwar hatsarin a wata sanarwa ta hukuma.

Kara karanta wannan
N70000 ta yi kadan: NLC za ta sake zama da Tinubu kan sabon mafi karancin albashi

Source: Original
Zargin da mazauna yankin ke yi
Ko da yake wasu mazauna yankin sun yi hasashen cewa ‘yan bindiga ne suka harbo jirgin, rundunar NAF ta bayyana cewa ana ci gaba da binciken musabbabin hatsarin.
Binciken ya nuna cewa hatsarin ya faru ne a kusa da Chukuba a Shiroro, ba a Zungeru ba kamar yadda aka yi iƙirari a bidiyon.
Saboda haka, an samu bayanan hatsarurrukan jiragen NAF a shekarun 2023 da 2025, amma babu wata hujja da ke tabbatar da ikirarin da aka yada a shekarar 2026.
Jirgin sojoji ya fado a Niger
Mun ba ku labarin cewa rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin yaki marar matuƙi na Rundunar Sojojin Sama ya faɗi a dajin jihar Niger.
Hatsarin ya faru ƙasa da sa’o’i 48 bayan ’yan ta’adda sun kashe manoma biyu tare da ƙona gidaje 13 a jihar.
Rundunar Sojojin Sama ta ce babu asarar rayuka, kuma ayyukan yaƙi da ta’addanci na ci gaba ba tare da tangarɗa ba.
Asali: Legit.ng