Amurka ta kashe babban kwamandan sojin Iran

Amurka ta kashe babban kwamandan sojin Iran

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa kasar Amurka ta kashe babban kwamandan dakarun sojojin juyin-juya hali na kasar Iran, Qasem Soleimani a wani harin sama da sojojinta suka kai filin jirgin sama na Bagadaza, a kasar Iraki.

Ma’aikatar tsaron Amurka, Pentagon ta bayyana cewa Shugaban kasar Donald Trump ne ya bayar da unurnin halaka kwamandan, wanda a cewarta yana ya kokarin shirya yadda zai a kaiwa Amurkawan Iraki da kuma yankin gaba daya hari.

Hedkwatar tsaron ta kuma bayyana cewa harin wani jan kunne ne, na duk wani hari da Iran za ta yi tunanin kai wa Amurka.

Shugaban Amurka, Trump ya aika sako na wani babban hoton tutar Amurka a shafinsa na Twitter.

KU KARANTA KUMA: Tirkashi: Mata ta sayar da mijinta sukutum akan N6,000, ta siyawa 'ya'yanta kayan sawa

Janar din shi ne babban mai tsara dabaru na Iran a kan Iraki, inda ake kallonsa a matsayin babban mai tsara hare-hare da ayyukan kungiyoyin mayakan sa kai da Iran ke mara wa baya a Syria da Lebanon.

Kasashen Larabawa na daukarsa a matsayin wani shu'umi da ke iya bayyana a ko'ina kuma a ko da yaushe.

Ministan harkokin waje na Iran Javad Zarif ya bayyana kisan Janar Soleimani a matsayin wata tsokana mai hadarin gaske.

Ya ce ya zama dole Amurka ta dandana kudarta kan abin da ya kira kasassabarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel