Kuma dai: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 5 a Taraba

Kuma dai: Yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 5 a Taraba

Wasu yan bindiga sun yi garkuwa da mutane biyar a karamar hukumar Gassol da ke jihar Taraba. Lamarin a cewar idon shaida ya faru a tsakanin Sabongida zuwa WuroJam a karamar hukumar Gassol da ke jihar Taraba a ranar Laraba, 1 ga watan Janairu.

Wani idon shaida Musa Sabongida ya bayyana cewa an yi garkuwa a mutanen ne a wani daji yayinda suke dawowa daga garin Tella da misalin karfe 5:00pm.

Ya bayar da sunayen wadanda aka sace a matsayin Hambali Haladu,Abdu Ibrahim, Buhari Abdu,Gidado Mallam Manu da Thomas Ernan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an fara tattaunawa tsakanin masu garkuwan da yan uwan wadanda aka sacen.

Ya ce tsakanin watannin Janairu zuwa Disamban da ya gabata an sace sama da mutane 70 a Sabongida, Tella, Sansani, Dubele, Yarima, Gassol, Wuriyo da Dananacha da sauran kauyuka a karamar hukumar Gassol.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari Kogi, sun kashe mutum 19 sannan sun kona gidaje da fadar sarki

Da aka tuntubi kakakin yan sandan jihar, DSP David Misal ya ce rahoton sace mutanen biyar bai iso ofishinsa ba.

A wani labari makamancin haka mun ji cewa masu garkuwa da mutane sun sace wasu ‘yan biyu a kauyen Gizawa dake karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina. An gano cewa ‘yan bindigar sun hari garin ne a sa’o’in farko na jiya a lokacin da mazauna garin ke bacci.

Majiyoyi da dama sun ce masu garkuwa da mutanen sun fito da Hassan da Hussaina Idris ta karfin tsiya daga dakunansu.

Hakazalika, an gano cewa wasu ‘yan bindiga sun hari gidan wani Magaji Abu a kauyen Badole, inda suka yi awon gaba da shanayensa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel