Nnamdi Kanu na Tsare a Gidan Yari, IPOB Ta Rufe Ofishin Shugaban Biafra
- IPOB ta dakatar da ofishin shugabanta da mukamin Daraktan Radio Biafra da Nnamdi Kanu ke rike da su har sai abin da hali ya yi
- Kungiyar ta ce matakin zai hana wasu amfani da sunan IPOB wajen aikata laifuffuka ko daukar matakan da ba a amince da su ba
- IPOB, mai rajin kafa Biafra ta bayyana cewa ba za ta dauki alhakin ayyukan mutanen da ba su da mukami ko izinin wakiltar kungiyar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB ta sanar da dakatar da ofishin shugabanta da kuma mukamin Daraktan Radio Biafra, wadanda Mazi Nnamdi Kanu ya ke rike da su a baya.
A cikin wata sanarwa da shugaban DOS na IPOB, Mazi Chikadibia Edoziem, ya fitar ranar Juma’a, kungiyar ta ce an dauki matakin ne domin kare ayyukanta da manufofinta, da kuma tabbatar da tsaron mambobinta.

Source: Getty Images
Dalilin dakatar da mukamin Nnamdi Kanu
A cikin sanarwar, kungiyar ta bayyana cewa tana da nauyin kare ayyukanta da kuma tabbatar da tsaron mambobinta a sassa daban-daban na duniya, musamman a yankunan da take da mabiya a Biafra, in jirahoton Tribune.
Ta ce dakatar da wadannan mukamai zai taimaka wajen hana duk wani gibi na tsaro ko rikicin gaggawa da ka iya tasowa sakamakon wasu ayyuka da ake dangantawa da kungiyar.
“Bisa la’akari da nauyin da ya rataya a wuyan shugabancin IPOB na kare manufofi da ayyukan kungiyar tare da kare mambobinta, an dakatar da ofishin shugabancin IPOB da kuma mukamin Daraktan Radio Biafra har sai abin da hali ya yi,” in ji sanarwar.
Kungiyar ta kara da cewa matakin zai taimaka wajen hana wasu mutane ko kungiyoyi da ba su da alaka da IPOB amfani da sunan kungiyar wajen gudanar da ayyukan da ba su dace da manufofinta ba.
IPOB ta nesanta kanta daga ayyukan wasu
DOS ta bayyana cewa akwai wasu mutane da kungiyoyi da ke ikirarin samun hurumi daga IPOB domin gudanar da ayyuka ko bayar da umarni da ba su da amincewar kungiyar.
A cewarta, dakatar da ofishin shugabancin zai taimaka wajen dakile irin wadannan ikirari da kuma hana daukar matakai ba tare da sahalewar shugabancin kungiyar ba.
Kungiyar ta ce duk wani laifi ko aiki da aka aikata da sunan ofishin shugabancin da aka dakatar daga yanzu ba za a dauke shi a matsayin aikin IPOB ba.
Ta bayyana cewa alhakin irin wadannan ayyuka zai rataya ne kawai a kan mutanen da suka aikata su, in ji rahoton The Guardian.

Source: Getty Images
Fargabar kame da kisan matasa
IPOB ta ce daya daga cikin abubuwan da suka sa aka dauki wannan mataki shi ne kare rayukan matasan da ke goyon bayan fafutukar Biafra.
Kungiyar ta yi zargin cewa wasu kalamai da ayyuka da ake yi ba tare da izini ba na iya jawo kama mutane, azabtarwa ko ma rasa rayuka.

Kara karanta wannan
N70000 ta yi kadan: NLC za ta sake zama da Tinubu kan sabon mafi karancin albashi
A cewarta, dakatar da wadannan mukamai zai taimaka wajen hana duk wani rudani da zai iya jefa matasa cikin hadari.
INEC ta taba yi wa Tinubu gargadi
A wani labari, mun ruwaito cewa, Kungiyar IPOB ta gargadi shugaban kasa Bola Tinubu da ya cire sunanta a matsayin ‘yan ta’adda ko kuma ya fuskanci shari’a.
Wannan na zuwa ne bayan Mai Shari’a, Abdul Kafarati ya ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta ta’addanci a ranar 20 ga watan Satumban 2017, Legit ta tattaro.
IPOB ta yi zargin cewa gwamnatin da alkalai na tsoron ganawa da lauyoyinta yayin da suke jiransu a kotun don ci gaba daga inda aka tsaya a shari’ar.
Asali: Legit.ng

