Yanzu Yanzu: DSS ta kama mutumin da ya shirya tare da yada bidiyon auren Buhari na bogi

Yanzu Yanzu: DSS ta kama mutumin da ya shirya tare da yada bidiyon auren Buhari na bogi

Rahotanni sun kawo cewa an cafke wani mutum da ake zargi da hadawa tare da yada bidiyon aure na bogi tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministarsa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa rundunar tsaro na farin kaya ce ta kama mutumin wanda zuwa yanzu ba a bayyana shi ba a ranar Juma’a, 3 ga watan Janairu.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton ana zuba idon jin bayani daga mahukunta na rundunar.

A ranar 10 ga watan Oktoba, Legit.ng ta ruwaito wani labarin kafofin sadarwa da ya shahara game da ikirarin cewa Shugaban kasa Buhari na shirin auren Hajiya Sadiya Umar Farouq, ministar harkokin agaji, kare annoba da ci gaban jama’a, a matsayin mata ta biyu.

Sakamakon haka, yan Najeriya da dama suka je masallacin Aso Rock, Abuja yan kwanaki kadan da jin yaduwar labarin.

Rahotanni sun ce masallacin a wancan ranar, ya cika da mutane, inda wasu masu bauta ke ta zumudin tabbatar da gaskiyar labari game da auran.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari Kogi, sun kashe mutum 19 sannan sun kona gidaje da fadar sarki

Femi Adesina, kakakin shugaban kasar ya fito ya karyata rahoton sannan ya bayyana shi a matsayin yaudara daga wadanda suka shirya shi.

Adesina ya kuma tabbatar da cewar babu wani biki dake gudana a fadar shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel