An Jibge Jami'an Tsaro, Sun Hana Mutane Zirga Zirga a Kananan Hukumomi 2 a Jihar Kano
- Rundunar ‘yan sandan Kano ta sanya dokar hana zirga-zirga a kananan hukumomin Dawakin Kudu da Warawa da ke jihar
- Dokar za ta fara aiki daga karfe 12:00 na rana zuwa 5:00 na yammacin gobe Asabar, 20 ga Yuni, 2026 saboda zaben cike gurbi
- Ma’aikatan INEC, jami’an tsaro, masu sa ido kan zabe da ‘yan jarida masu izini ne kawai aka keɓance daga wannan doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sa dokar hana zirga-zirga a Kananan Hukumomin Dawakin Kudu da Warawa gabanin zaben cike gurbin dan Majalisar Wakilai da za a gudanar ranar Asabar.
Rundunar ta ce za a aiwatar da dokar daga karfe 12:00 na rana zuwa karfe 5:00 na yamma ranar 20 ga Yuni, 2026, domin tabbatar da zaman lafiya da gudanar da sahihin zabe.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta ce hakan na kunshe ne a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a madadin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ibrahim Adamu Bakori.
'Yan sanda sun kebance wasu mutane
Sanarwar ta ce dokar ta shafi kowa amma ban da jami’an tsaro, ma’aikatan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), masu sa ido kan zabe da aka tantance da ‘yan jarida masu sahihin shaidar aiki
Rundunar ta bayyana cewa an jibge jami’an tsaro a rumfunan zabe, cibiyoyin tattara sakamako, ofisoshin INEC da sauran muhimman wurare a yankunan da abin ya shafa.
CP Bakori ya ce matakan tsaron sun samo asali ne daga shawarwarin kwamitin hadin gwiwa na tsaro kan zabe.
“Mun samar da cikakken tsarin tsaro tare da hadin gwiwar dukkan hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da zaman lafiya da sahihin zabe,” in ji shi.
Gargadi kan laifuffukan zabe
Kwamishinan ya bukaci masu kada kuri’a su kasance masu bin doka da oda yayin gudanar da zaben, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Ya kuma gargadi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da kada su yi kamfe ko nuna alamun jam’iyya a cikin tazarar mita 300 daga rumfunan zabe.
Bakori ya jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci sayen kuri’u, sayar da kuri’u, kwace akwatunan zabe, tsoratar da masu kada kuri’a da yada labaran karya ko bayanan bogi ba.
“Duk wanda aka kama da aikata wani laifin zabe za a kama shi tare da gurfanar da shi bisa tanadin Dokar Zabe ta Najeriya,” in ji Bakori.

Source: Facebook
'Yan sanda sun ja hankalin jama'a
Kwamishinan ya tabbatar da cewa an samar da isasshen tsaro ga jami’an zabe, kayan aiki da cibiyoyin tattara sakamako kafin, lokacin da kuma bayan zaben.
Ya kuma bukaci mazauna yankin su rika kai rahoton duk wani abu da ya tayar musu da hankali ga jami’an tsaro.

Kara karanta wannan
Jerin gwamnonin jihar Ekiti daga 1999 zuwa yau yayin da ake shirin sabon zabe a 2026
Rundunar ta kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa, ‘yan takara da magoya bayansu da su mutunta doka domin tabbatar da gudanar da zaben cikin lumana.
'Yan sanda sun kara kaimi a Kano
A wani labarin, kun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama mutane 345 da ake zargi da aikata laifuffuka tare da kwato makamai 270 masu haɗari.
Dakarun rundunar sun yi haka ne a wani samame na tsaro da aka gudanar na tsawon kwanaki uku a dukkan ƙananan hukumomin jihar.
Hakan na zuwa ne yayin da 'yan daba ke cigaba da tare hanyoyi a Kano da sace-sacen kayayyaki a kasuwanni da sauransu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

