APC Ta Yi Magana da 'Yan Majalisa Suka Fara Maganar Tinubu Ya Sauka

APC Ta Yi Magana da 'Yan Majalisa Suka Fara Maganar Tinubu Ya Sauka

  • Jam'iyyar APC mai mulki ta soki jam’iyyun adawa bisa goyon bayan kiran Bola Tinubu ya sauka daga mulki saboda matsalolin tsaro da suka addabi Najeriya
  • Wasu 'yan majalisar wakilai sun bukaci shugaba Tinubu ya dakatar da harkokin 2027 tare da ƙaddamar da shiri na wata shida kan tsaro da tattalin arziki
  • Sai dai jam’iyyar APC ta jaddada cewa gwamnatin Tinubu na ɗaukar matakan da suka dace domin magance ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta a yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta yi Allah-wadai da jam’iyyun adawa da suka hada da ADC, PDP, SDP, NDC da wasu, bisa goyon bayan cewa Bola Tinubu ya yi murabus.

An fara maganar Tinubu ya sauka ne saboda tabarbarewar matsalar tsaro a ƙasar amma APC ta bayyana bukatar a matsayin wanda siyasa ta haifar.

Kara karanta wannan

CUPP ta goyi bayan wasu yan majalisa da suka ba Shugaba Tinubu zabi 1 ko ya yi murabus

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a lokacin da ya ke wani jawabi. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa a ranar Laraba, marasa rinjaye a majalisar wakilai suka yi kakkausar suka kan halin da ƙasar ke ciki tare da zargin gwamnatin shugaba Tinubu da kasa magance matsalar tsaro.

Korafin da aka yi kan tsaro

Da yake magana da manema labarai a harabar majalisar dokoki ta kasa da ke Abuja, shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Fred Agbedi, ya ce ƙasar na fuskantar mafi munin yanayi tun 1999.

Agbedi ya ce:

“Ya kamata shugaba Tinubu ya dakatar da duk wasu harkokin siyasar 2027 sannan ya ayyana wani shirin watanni shida na farfaɗo da tsaro da tattalin arziki.”

Agbedi ya kuma bayyana cewa tsananin matsin tattalin arziki da rashin tsaro alamu ne da ke nuna cewa Najeriya na dab da zama ƙasar da kamar ba gwamnati.

A kan haka kuma ya ƙalubalanci shugaban kasa Bola Tinubu da ya samar da ingantaccen jagoranci ko kuma ya sauka daga mulki.

Kara karanta wannan

An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya

Jam'iyyar APC ta kare Bola Tinubu

Daraktan yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, ya yi watsi da kiran Tinubu ya yi murabus, yana mai bayyana kiran da kuma zargin cewa Najeriya na dab da zama kamar ba gwamnati a matsayin rashin hankali.

Punch ta rahoto Bala Ibrahim ya ce shugaban kasa na ci gaba da mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro da kuma farfaɗo da tattalin arziki.

Ya kafa hujja da cewa ba Najeriya ce kadai ke fama da matsalolin tsaro da tattalin arziki ba, yana mai cewa ƙasashe kamar Amurka da Birtaniya ma suna fuskantar irin waɗannan ƙalubale.

Rarara ya yi magana kan tsaro

A wani labarin, kun ji cewa mawakin APC, Dauda Kahutu Rarara ya magana kan yanayin tsaron Najeriya, musamman kan sace dalibai a makarantu.

Rarara ya yi kira ga jama'a da su daina yada bidiyon 'yan ta'adda a kafafen yada labarai domin hakan zai iya zama kara masu karfi ba tare da an sani ba.

Mawakin ya yi kira ga malaman addini da su daina neman suna wajen yin wa'azi kan tsaro, inda ya ce ya kamata su fara yi wa 'yan soshiyal midiya nasiha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng