Rundunar sojin sama ta yi kasa-kasa da gine-ginen yan Boko Haram a dajin Sambisa
Rundunar sojin sama na Najeriya ta lalata wani ginin ajiye kayayyakin jin dadi na yan ta’addan Boko Haram a Gujeri da ke dajin Sambisa a jihar Borno.
Rundunar ta ce an aiwatar da aikin ne ta jirgin yakin dakarun Operation Lafiya Dole.
Air Commodore Ibikunle Daramola, daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin sama ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki a ranar Juma’a, 3 ga watan Janairu.
Ya yi bayanin cewa an cimma wannan nasarar ne a wani farmakin dare da aka kai a ranar 31 ga watan Disamba, 2019 wanda ya biyo bayan wasu bayanan kwararu.
Daramola ya ce sashin kwararru na ISR sun gano wasu gine-gine a karkashin wasu bishiyoyi a wajen wadan yan ta’addan ke amfani da su wajen ajiye man fetur da sauran kayayyakin kula da ababen hawansu.
“Don haka, rundunar ta tura jiragenta domin kai hari wajen wanda hakan ya yi sanadiyar lalata gine-ginen ajiyar kayayyakin da kuma wasu gine-gine a sansanin,” inji shi.
KU KARANTA KUMA: Masu so nayi murabus na bakin ciki da nasarorin da na samu ne – Oshiomhole
Daramola ya ce rundunar sojin saman wacce ke aiki tare da sauran rundunar kasa, za su cigaba da kokarinsu na kawo karshen dukkanin yan ta’addan da suka saura a arewa maso gabas.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng