Bola Tinubu Ya Sake Tsawaita Wa'adin Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya

Bola Tinubu Ya Sake Tsawaita Wa'adin Shugaban Hukumar Kwastam Ta Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa’adin aikin shugaban Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi, da watanni shida
  • Adeniyi zai jagoranci ɗaga matsayin jami’an da suka cancanta tare da kula da ritayar waɗanda suka kai shekaru 60 ko suka yi shekaru 35 a aiki
  • An naɗa shi shugaban Hukumar Kwastam a watan Yunin 2023, sannan aka tabbatar da shi a matsayin cikakken shugaba a Oktoba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙara tsawaita wa’adin aikin shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS), Adewale Adeniyi, da watanni shida.

Wannan mataki na zuwa ne yayin da wa'din shekara guda da Shugaba Bola Tinubu ya kara masa a bara ke dab da karewa.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana sa hannu a takardun aiki a Aso Rock Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Dalilin karawa shugaban kwastam wa'adi

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, 19 ga watan Yuni, 2026.

Kara karanta wannan

Dalilai 3 da za su iya sanya APC lashe zaben gwamnan Ekiti na 2026

A cewar Bayo Onanuga, wa’adin da aka ƙara wa Adeniyi na shekara daya a watan Yulin 2025 zai kare ne a ranar 1 ga Agustan 2026.

Ya ce sabon ƙarin wa’adin na watanni shida, wanda zai ƙare a watan Fabrairun 2027, zai ba Adeniyi damar ƙarfafa aiwatar da tsare-tsaren gwamnati tare da tabbatar da sauyin shugabanci cikin tsari.

Ayyukan da ke gaban shugaban kwastam

Sanarwar ta ce a lokacin wannan ƙarin wa’adi, Adeniyi zai yi aiki tare da Hukumar Gudanarwar Kwastam domin tabbatar da ɗaga matsayin jami’an da suka cancanta zuwa mukamin Kwanturola na Kwastam.

Haka kuma zai kula da ritayar dole ga jami’an da suka kai shekaru 60 ko kuma waɗanda suka yi shekaru 35 suna aikin gwamnati.

Yadda ya shiga aikin Kwastam

Adeniyi ya shiga Hukumar Kwastam ta Najeriya ne bayan kammala karatunsa a Jami’ar Obafemi Awolowo a ƙarshen shekarun 1980.

Ya yi ta hawa matakan aiki har ya zama Mataimakin Kwanturola a shekarar 2012, sannan Kwanturola a 2017.

A shekarar 2020 ya zama Mataimakin Babban Kwanturola Janar, kafin a naɗa shi Mukaddashin Kwanturola Janar a watan Janairun 2023.

Kara karanta wannan

Roko na musamman da Sarki Sanusi II ya yi ga kungiyar EU game da Kano

Daga bisani, Shugaba Tinubu ya naɗa shi Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam a watan Yunin 2023.

Tinubu ya tabbatar da naɗinsa a 2023

A ranar 19 ga Oktoban 2023, Shugaba Tinubu ya tabbatar da Adeniyi a matsayin cikakken Babban Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam.

Kafin haka, yana riƙe da mukamin ne a matsayin mukaddashi bayan ya karɓi ragamar shugabancin hukumar daga tsohon shugaban Kwastam, Hameed Ali, a watan Yunin 2023.

Adewale.
Shugaban hukumr kwastam ta Najeriya, Adewale Adeniyi Hoto: @CustomsNG
Source: Twitter

Tun da farko, wa’adinsa zai ƙare ne a ranar 31 ga Agustan 2025 bayan cika shekaru 35 yana aiki, amma shugaban ƙasa ya ƙara masa shekara guda, wadda ake sa ran za ta ƙare a watan Agustan 2026.

Kwastam ta kawo tsarin gwajin kwaya

A wani labarin, kun ji cewa hukumar kwastam ta shirya yaki da matsalar ta'ammali da miyagun kwayoyi daga wajen jami'an da ke aiki a karkashinta.

Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana cewa ba za su lamunci ma'aikata na aiki a cikin yanayi mara kyau ba.

Ya umarci cewa a rika gudanar da gwajin miyagun kwayoyi ga sababbin ma’aikata da kuma jami’an da ke aiki a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262