Dakarun Hisbah Sun Kai Samame, Sun Kama 'Yan Mata da Samari Suna Baɗala a Kano

Dakarun Hisbah Sun Kai Samame, Sun Kama 'Yan Mata da Samari Suna Baɗala a Kano

  • Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta gudanar da wani samame, inda ta kama matasa maza da mata 16 bisa zargin aikata ayyukan badala
  • Hisbah ta bayyana cewa matasan sun shiga hannu ne a samamen da ta kai yankin El-Kanemy Suite, titin BUK, Danbare da Layin Shisha
  • Hukumar ta ce ana yi wa wadanda aka kama wa'azi da shawarwari kafin sakin su bayan sun tabbatar da cewa ba za su sake aikata laifi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mutane 16 a wani samame da ta kai domin dakile ayyukan da ta bayyana a matsayin na marasa da'a a wasu sassan jihar.

Dakarun rundunar ta Hisbah sun gudanar da samamen ne a El-Kanemy Suite da ke kan titin Yahaya Gusau, da kuma yankunan jami'ar BUK Road, Danbare da Layin Shisha.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci za a rataye jagoran dabar yan bindiga Jibrin Halilu har lahira

Hisbah.
Dakarun rundunar Hisbah da ke aikin gyara tarbiyya a jihar Kano Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Twitter

Hisbah ta kama mata da maza 16

Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar, Mujahiddeen Aminuddeen, ne ya tabbatar da kama mutanen yayin da yake zantawa da jaridar Daily Trust ranar Alhamis.

Aminuddeen ya ce wadanda jami'an hukumar suka kama yayin samamen sun kunshi maza shida da mata 10.

Ya bayyana cewa a halin yanzu dukkansu suna hannun hukumar Hisbah domin karbar shawarwari da wa'azi.

Matakin da Hisbah za ta dauka kansu

“Dukkan wadanda muka kama suna hannun hukumar Hisbah yanzu haka, inda ake yi musu nasiha. Wannan ne karo na farko da aka kama su.
"Muna yi musu wa'azi, kuma za mu gayyaci 'yan uwansu tare da ba su shawarwari. Daga nan sai su rattaba hannu kan alkawarin cewa ba za su sake aikata irin wadannan abubuwa ba,” in ji shi.

Mataimaakin kwamandan ya kara da cewa hukumar Hisbah za ta ci gaba da sanya ido kan wadanda aka kama bayan an sake su domin tabbatar da sun gyara halayensu.

Kara karanta wannan

An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya

Manufar ayyukan da Hisbah ke yi

Ya ce manufar hakan ita ce karfafa musu gwiwar rungumar kyawawan dabi'u da kuma kauce wa abubuwan da suka saba wa dokoki da ka'idojin zamantakewa.

Hukumar Hisbah ta Kano na da alhakin kula da aiwatar da wasu dokoki da ka'idojin addinin Musulunci a jihar, kamar yadda Aminiya ta kawo.

Daurawa.
Babban kwamandan Hisbah na jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Hoto: Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

A kai a kai hukumar kan gudanar da samame domin dakile ayyukan da take ganin sun saba wa tsarin da'a da tarbiyya, ciki har da shan giya, karuwanci da sauran dabi'un da take kallon ba su dace da al'adun al'umma da addininsu ba.

Hisbah ta fara shirye-shiryen auren gata

A baya, kun ji cewa hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kammala shirye-shiryen gudanar da gwajin lafiya a kan ma’aurata 3,000 da ake sa ran za su amfana da shirin auren gata.

Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahedeen Aminudeen, ya ce za a fara gudanar da gwajin lafiyar ne daga ranar Litinin, 8 ga watan Yunin 2026, a ƙananan hukumomi 24 na jihar Kano.

Ya ce ma’auratan sun haɗa da mata 1,500 da maza 1,500 waɗanda za a yi masu gwaje-gwajen lafiya na dole domin tabbatar da yanayin lafiyarsu kafin a ba su damar shiga shirin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262