Masu so nayi murabus na bakin ciki da nasarorin da na samu ne – Oshiomhole

Masu so nayi murabus na bakin ciki da nasarorin da na samu ne – Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Kwamrad Adams Oshiomhole ya bayyana cewa masu neman ya yi murabus hassada da bakin ciki suke yi masa, ganin cewa ya taka rawar ganin da ba a taba takawa ba a jam’iyyar.

A cewar Oshiomhole wadannan tarin nasarorin da ya samu ne yasa wasu suke ganin ba yadda suke so ba yayi.

Oshiomhole ya ce: “Idan kaga yara na jifa a itace to sun hango nunannen mangwaro ne. Ammma haka kawai ba za su rika jifar itacen kwakwan da ba shi da ‘ya’ya ba.” A dililin haka yasa ake cakalar sa ta ko-ina.

“Mutane sun san yadda muka iske jam’iyyar APC a lokacin da aka zabe mu a 2018. Yanzu akwai tazara sosai da muka ba wadanda suka shugabanci jam’iyyar a baya.

“Ana rantsar da mu muku tunkari zaben Ekiti da ke hannun PDP. Yanzu gwamna Fayemi ne gwamna a jihar. haka muka yi wa sauran zabubbukan da muka yi.

“A zaben 2015, idan baku manta ba tazarar da shugaba Buhari ya ba Goodluck Jonathan na jam’iyyar PDP kuri’u miliyan uku da ya doriya ne, amma a 2019, mun ba PDP tazarar kuri’u sama da miliyan hudu ne.

“Baya ga haka mun taka rawar gani matuka a wajen zaben shugabannin majalisar Tarayyya da na Dattawa. A baya kiri=kiri PDP ta dauke kujerar mataimakin shugaban majalisa muna gani babu yadda zamu saboda lalaci. Amma yanzu fa Kaf muna muke da kujerun duka.”

KU KARANTA KUMA: Tsohon kakakin majalisar dokokin Imo ya sauya sheka zuwa APC

Oshiomhole ya yi wannan kalamai ne a yayinda ya ke mika rahotan ayyukan jam’iyyar tun bayan rantsar da ita da aka yi a 2018 ga kwamitin zartaswar jam’iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng