Mafi karancin albashi: Malaman makaranta a Kano sun koka

Mafi karancin albashi: Malaman makaranta a Kano sun koka

Rahotanni sun kawo cewa wasu malaman makarantun Firamare na jihar Kano sun koka kan cewa har yanzu ikirarin da gwamnatin jihar ke yin a cewar ta fara aiwatar da sabon karancin albashi na 30,000 bai iso wajensu ba.

Kafar labarai ta BBC Hausa ta ruwaito cewa a maimakon haka malaman sun yi cewa ragi aka yi musu a albashin maimakon kari.

Majiyar tamu ta ruwaito ina wani malami ke fadin cewa "mun ji an ce an samu karin amma ni rabin nawa na da na samu saboda haka ina kira ga gwamnati da ta duba yanayin da muke ciki ta yi abin da ya kamata."

Har ila yau wata malama ta ce "suna ta cin burin sayen mota amma sai ga shi naira 3,000 kawai ta gani a kan albashin nata."

To sai dai kungiyoyin kwadago sun ce sun fara tattauna wa da mahukunta domin shawo kan matsalar.

Shugaban kungiyar kwadago na jihar Kano, Kwamrad Kabiru Minjibir ya ce sun samu labarin korafin malaman makarantar sannan cewa suna duba hanyar warware matsalar.

KU KARANTA KUMA: A karshe: Wanda ya kitsa fashin bankin Abuja ya shiga hannu

Ita ma gwamnatin jihar Kano, ta bakin Murtala Sule Garo, kwamishinan kananan hukumomi, ta ce ita ma tana kokarin gano abin da ya jinkirta biyan malaman makarantun Firamare sabon albashin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel