Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari Kogi, sun kashe mutum 19 sannan sun kona gidaje da fadar sarki

Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun kai hari Kogi, sun kashe mutum 19 sannan sun kona gidaje da fadar sarki

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga sun kashe akalla mutane 19 a garin Tawari a dake karamar hukumar Kogi, jihar Kogi inda suka kona wasu gine-gine ciki harda faar sarkin garin.

Kakakin yan sandan jihar Kogi, Mista Williams Anya, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Lokoja a ranar Juma’a, 3 ga watan Janairu.

Ya bayyana cewa tawagar yan sanda sun ziyarci garin sannan cewa an kona gine-gine da dama ciki harda wuraren bauta.

Garin Tawari na yan kilomita kadan da garin Geru a hanyar babban titin Lokoja-Abuja.

Wata mazauniyar Tawari, Misis Comfort Solomon, wacce ta yi nasarar tsira aga harin, ta bayyana cewa yan bindiga kimanin su 100 sun kai mamaya garin a aren ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Rundunar sojin sama ta yi kasa-kasa da gine-ginen yan Boko Haram a dajin Sambisa

Ta ce yan binigan sun zo ne a kan Babura sannan suka farma kauyen, ina suka ta kashe-kashe da kone-konen gidaje har zuwa safiyar ranar Juma’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel