Kotu a Kano Ta Yanke wa Wata Mata Hukunci kan Safarar Makamai ga 'Yan Bindiga
- Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke wa Raya Haruna hukuncin daurin shekaru 10 kan safarar makamai ga ‘yan bindiga
- Alkalin kotun ya ce ko da ba ta shiga kai tsaye a hare-hare ba, rawar da ta taka ta taimaka wajen karfafa ayyukan ta’addanci
- An kama matar ne a 2024 yayin wani samame da jami’an tsaro suka gudanar domin dakile safarar makamai zuwa hannun ‘yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta yanke wa wata mata mai suna Raya Haruna hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari.
An yanke wa Raya Haruna hukuncin ne bayan samunta da laifin safarar makamai da harsasai ga ‘yan bindigar da ke addabar wasu yankunan Arewacin Najeriya.

Source: Getty Images
Laifuffukan da aka tuhumar Raya da aikatawa

Kara karanta wannan
Battujo: Kotu ta yanke wa mahaifiyar ƙasurgumin dan bindiga da 'yar'uwarsa hukunci
Mai shari’a Simon Amobeda ne ya yanke hukuncin a ranar Juma’a bayan kotun ta tabbatar da cewa an same ta da laifi dumu dumu a tuhume-tuhume uku, in ji rahoton Punch.
Tuhumen tuhume uku da masu kara suka shigar kan Raya sun shafi safarar bindigogi ba bisa ka’ida ba da kuma bayar da tallafin da ya taimaka wa kungiyoyin masu aikata laifuka.
Dokar Najeriya ta haramta mallaka, safara ko samar da makamai ba bisa ka’ida ba, tare da haramta duk wani tallafi ko taimako da zai iya karfafa ayyukan kungiyoyin ta’addanci ko masu aikata manyan laifuffuka.
Masu gabatar da kara sun bayyana cewa matar ta shiga cikin harkar jigilar makamai da harsasai zuwa ga wasu kungiyoyin ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a wasu sassan Kano da jihohin da ke makwabtaka da ita.
Yadda aka kama Raya Haruna
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro sun kama Raya Haruna ne a shekarar 2024 yayin wani samame na musamman da aka kaddamar domin dakile safarar makamai zuwa hannun ‘yan bindigar da ke tada kayar baya a yankin.
Tun bayan kama ta, ta ci gaba da kasancewa a tsare yayin da ake gudanar da shari’ar a gaban kotun tarayya, in ji rahoton AIT.

Source: Original
Hukuncin da kotu ta yanke wa Raya
Yayin da yake yanke hukunci, Mai shari’a Simon Amobeda ya bayyana cewa ko da yake ba a tabbatar da cewa matar ta shiga kai tsaye cikin hare-haren ‘yan bindiga ko ta taba amfani da makami wajen kashe mutane ba, rawar da ta taka wajen safarar makamai na da matukar tasiri wajen ci gaba da ayyukan ta’addanci.
Alkalin ya ce samar da makamai da harsasai wani muhimmin bangare ne da ke bai wa kungiyoyin masu aikata laifuka damar kai hare-hare, haddasa asarar rayuka, jikkata mutane da kuma lalata dukiyoyi.
A cewarsa, duk wanda ya taimaka wajen samar da irin wadannan kayayyaki ga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga yana taka rawa kai tsaye wajen ci gaba da matsalar tsaro.
An yanke wa wata mata hukuncin kisa
A wani labari, mun ruwaito cewa, kotun tarayya da ke Katsina ta yankewa Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin ta’addanci.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto mutanen da aka gani a bidiyo tare da Janar Rabe a hannun 'yan bindiga
Kotun ta samu matar da laifin safarar harsasai 438 zuwa wani shugaban ‘yan bindiga da ke maboyarsa a dajin Dunburum.
Hukumar DSS ta kama Hauwa’u Mukhtar a tashar mota ta Jibia a shekarar 2023 yayin da ake zargin tana kai harsasai Zamfara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
