Fasto Bakare ya bayyana ainahin makiyan Najeriya

Fasto Bakare ya bayyana ainahin makiyan Najeriya

Fasto Tunde Bakare, Shugaban cocin Latter Rain Assembly, a ranar Lahadi, 5 ga watan Janairu ya jero wasu mutane da ya bayyana a matsayin ainahin makiyan Najeriya.

Babban Faston ya yi jawabin ne yayinda yake bayyana ra’ayinsa a kan halin da kasar ke ciki.

Bakare ya ce ana samun ainahin makiya na gaskiya a kowani mataki na gwamnati, daga karamar hukuma zuwa jihar har ya kai ga matakin tarayya, da kuma dukkanin matakin gwamnati a Najeriya.

Faston ya bayyana cewa wadanda ke satar kudin kasa da kuma masu goyon bayansu sune ainahin makiya na gaskiya a cikin mutane.

Ya bukaci yan Najeriya a wannan sabuwar karni da su tashi tsaye domin juyawa ainahin makiya baya a dukkanin mataki na gwamnati maimakon sukar yan jaridan da ke caccakar gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Gwamnonin arewa sun gargadi gwamnatin tarayya kan janye dakarun soji

A baya mun ji cewa Fasto Tunde Bakare, ya ba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shawarar ya tsaida Magajinsa.

Faston da ya tsayawa Muhammadu Buhari a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar CPC a 2011, ya yi magana game da 2023.

Tunde Bakare ya roki ‘Yan Najeriya su yi addu’a ta yadda mulki ba zai koma hannun Barayi da Miyagu idan har Buhari ya kammala wa’adinsa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel