Shugabancin kasa: Har yanzu arewa na da sauran wa’adi daya - Owie

Shugabancin kasa: Har yanzu arewa na da sauran wa’adi daya - Owie

Wani tsohon bulaliyar majalisar dattawa, Roland Owie, a ranar Lahadi, 5 ga watan Janairu ya ce yankin Arewa za ta cigaba da rike mulki a 2023 don daidaito a lokacin da yankin kudu ta yi tana mulki tun 1999.

Owie, wanda ya zanta da manema labarai a gidansa da ke Benin, ya ce wannan shiri zai tabbatar da daidaito, adalci da kuma gaskiya.

Batun wanda zai yi shugabanci a 2023 ya kasance abun tattaunawa a tsakanin shugabannin siyasa a yankin kudu, wadanda tuni suka fara Kira ga mika mulki ga yankin kudancin Najeriya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gama wa’adinsa na biyu a 2023.

Amma Owie ya ce kudu ta fi arewa dadewa kan mulki tun 1999.

Owie ya kuma bayyana cewa “idan aka mika mulki ga kudu, bayan 2023, toh yankin kudu maso yamma ya kamata a ba."

KU KARANTA KUMA: Imo: ‘Ya ‘yan APC sun ce Ministan ilmi ya na yi wa Jam’iyya makarkashiya

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban cocin Latter Rain Assembly, Fasto Tunde Bakare, ya ba shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shawarar ya tsaida Magajinsa.

Faston da ya tsayawa Muhammadu Buhari a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar CPC a 2011, ya yi magana game da 2023.

Tunde Bakare ya roki ‘Yan Najeriya su yi addu’a ta yadda mulki ba zai koma hannun Barayi da Miyagu idan har Buhari ya kammala wa’adinsa ba.

A jawabinsa ga ‘Yan kasa, Malamin addinin Kiristar, ya yi kira ga shugaba Buhari ya kafa tubali masu karfi da za su sa nagari ya gaje sa a nan gaba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel