Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Abdulfatah Ahmed, tsohon gwamnan jihar Kwara ya karyata zargin da Gwamna Abdulrahman Abdulrazak ya yi a kan gwamnatinsa. Abdulrazak ya yi zargin cewa gwamnatin Ahmed ta siyar wa da abokai da makusanta kadarorin gwamnati guda 110.
Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya) ya bayyana cewa zamanin juyin mulki ya dade da wucewa a Najeriya, cewa lallai wawan soja ne kadai zai yi irin wannan yunkuri.
Hanan, daya daga cikin yaran Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta ce ta matsu ta sake samun wasu ayyukan karan kanta bayan na baya day a haifar da cece-kuce.
Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou ya daura sabon shugaban rundunar sojin kasar bayan kaddamar da munanan hare-hare biyu a kwanan nan wadanda suka yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 160.
Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, zai kaddamar da wasu manyan hanyoyi da Gwamna Abullahi Ganduje na jihar Kano ya yi aikinsu a ranar Litinin.
Rahotanni sun kawo cewa mutane biyu sun mutu a wani karo tsakanin makiyaya da manoma a Sobe, karamar hukumar Owan ta yamma da ke jihar Edo.
Rahotanni sun kawo cewa sanatocin sun nuna fushinsu a kan naira miliyan biyu da aka ba kowannensu a matsayin goron Kirsimeti. Harma an jiyo wasu sanatoci na bayyana kudin da aka basu a matsayin digo cikin tarin bukatunsu na Kirsi
Rahotanni sun kawo cewa wasu jami’an hukumar kwastam na Najeriya su biyu da aka yi garkuwa dasu sun kubuta daga hannun masu garkuwan bayan kwanaki hudu da sace su.
Wani bincike da kwamitin gwamnatin jihar Kano kan yaran da basa zuwa makaranta ya nuna cewa yawan yaran da ke zuwa makaranta ya karu a jihar, inda hakan ya rage adadin da aka samu a 2015 daga 1,306,106 zuwa 410,873.
Aisha Musa
Samu kari