Marasa zuwa Makaranta a Jihar Kano sun ragu da mutum kusan 1,000,000

Marasa zuwa Makaranta a Jihar Kano sun ragu da mutum kusan 1,000,000

Wani bincike da kwamitin gwamnatin jihar Kano kan yaran da basa zuwa makaranta ya nuna cewa yawan yaran da ke zuwa makaranta ya karu a jihar, inda hakan ya rage adadin da aka samu a 2015 daga 1,306,106 zuwa 410,873.

Ku tuna cewa a 2015 rahoton hukumar tattara bayanan ilimi ta kasa ya nuna cewa jihar ce ke da mafi yawan yara da basa zuwa makaranta inda yawansu ya kai 1,306,106.

A cewar rahoton, daga cikin yara 410,873 da basa zuwa makaranta a jihar, 275,917 maza ne, wanda hakan ya wakilci kaso 67 cikin 100 sannan 134,956 sun kasance mata wanda ke daidai da kaso 33 cikin 100.

Rahoton ya kuma nuna cewa karamar hukumar Tofa ce ke da mafi karancin yara da basa zuwa makaranta su 2,184 sannan Rogo ke da mafi yawan yara su 15,899.

Sai dai kuma a wata sanarwa daga Abba Anwar, babban sakataren Gwamna Abdullahi Ganduje, ya ce manufar gwamnan da matakinsa na son inganta ilimi ne ya taimaka wajen rage yawan yaran cikin yan shekaru kadan.

KU KARANTA KUMA: An kwantar da Gwamnan Bauchi a asibitin London saboda rashin lafiya

A cewarsa, wani manufa da ya haifar da hakan shine sanannen kudirin nan na jihar, wato bayar da ilimi kyauta da kuma wajabta karatun Firamare da Sakandare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel