Yanzu Yanzu: Buhari ya nada tsohon Shugaban DSS a matsayin Shugaban NISS

Yanzu Yanzu: Buhari ya nada tsohon Shugaban DSS a matsayin Shugaban NISS

- Shugaba Muhammadu Buhari ya nada tsohon Darakta Janar ba hukumar tsaro na farin kaya (DSS), A.A. Gadzama, a matsayin Shugaban makarantar tsaro na kasa (NISS)

- Nadin wanda ya fara aiki daga ranar 16 ga watan Disamba 2019 zai shafe tsawon shekaru hudu

- Hakan na kunshe ne a wani jawabi daga babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon Darakta Janar ba hukumar tsaro na farin kaya (DSS), A.A. Gadzama, a matsayin Shugaban makarantar tsaro na kasa wato National Institute for Security Studies (NISS).

Nadin wanda ya fara aiki daga ranar 16 ga watan Disamba 2019 na kunshe ne a wani jawabi daga babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha.

Nadin zai shafe tsawon shekaru hudu ne.

A wani labarin kuma, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa wasu kwamitoci guda biyu da zasu sanya idanu wajen gudanar da aikin samar da wutar Mamabilla na Megawatta 3050 a jahar Taraba, yankin Arewa ta tsakiya.

KU KARANTA KUMA: Gobara ta tashi a tsohuwar kasuwa a Sokoto

Kwamitocin guda biyu sun hada da kwamitin ministoci da zasu dinga tattaunawa tare da auna matsayin aikin a karkashin jagorancin ministan wutar lantarki, da kuma kwamitin tabbatar da an gudanar da aikin yadda ya kamata tare da kammala shi a lokacin daya dace.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel