Na siyar da kadarorin gwamnatin Kwara bisa ka’ida - Ahmed

Na siyar da kadarorin gwamnatin Kwara bisa ka’ida - Ahmed

Abdulfatah Ahmed, tsohon gwamnan jihar Kwara ya karyata zargin da Gwamna Abdulrahman Abdulrazak ya yi a kan gwamnatinsa.

Abdulrazak ya yi zargin cewa gwamnatin Ahmed ta siyar wa da abokai da makusanta kadarorin gwamnati guda 110 a lokacin da ta ke mulki.

Ahmed a wani jawabi daga hadiminsa, Muyideen Akorede ya karyata adadin da gwamnan Kwara ya bayyana.

Ya kuma wanke gwamnatinsa daga aikata kowani laifi game da siyar da kadarorin gwamnati.

Tsohon gwamnan ya ce lallai gwamnatinsa ta bi ka’ida wajen siyar wa da jami’an gwamnati da wasu mambobin majalisar dokokin jihar Kwara ta bakwai wasu gidajen din gwamnati.

Ya ci gaba da cewa hakan ya shafi sauran kayayyakin da gwamnatinsa ta batar inda aka biya kudin zuwa ga asusun gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Wawan soja ne kadai zai yi tunanin juyin mulki – IBB

A wani labari na daban, mun ji cewa fitaccen Masanin shari’ar nan, kuma gawurtaccen Mai kare hakkin Bil Adama, Femi Falana, ya maida martani ga fadar shugaban kasa.

Femi Falana ya yi raddi ne ga kalaman da Mai magana da yawun bakin shugaban kasa watau Graba Shehu ya yi a game da Hannan Buhari.

Malam Shehu ya fito ya na kare ‘Diyar shugaban kasar bayan ta yi amfani da jirgin gwamnati wajen yin wasu sabgoginta, ya ce ba ta yi laifi ba.

Sai dai Femi Falana SAN, ya bayyana cewa sam bai halatta ‘Diyar shugaban kasar Najeriyar ta yi amfani da jirgin fadar shugaban kasa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng