Shugaban Nijar ya tsige shugaban rundunar sojin kasar

Shugaban Nijar ya tsige shugaban rundunar sojin kasar

Shugaban kasar Nijar, Mahamadou Issoufou ya daura sabon shugaban rundunar sojin kasar bayan kaddamar da munanan hare-hare biyu a kwanan nan wadanda suka yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 160.

Ahmed Mohamed, tsohon Shugaban rundunar sojin kasar ya kwashe tsawon shekaru biyu yana jagorantar rundunar.

A yayinda ya ke shugabantar rundunar, samu karuwar gare-hare sosai a kasar musannan daga kungiyoyin yan ta’addan Boko Haram da kuma ISWAP.

A gyaran da shugaban Nijar din ya yi wa rundunar sojin kasar, ya tsige shugabanni uku.

Wadannan shugabanni da aka sauke sun hada da babban sakataren ofishin ministan tsaro, Shugaban hafsan sojojin kasar da kuma babban sufeton sojoji.

A yanzu haka an nada Birgediya Janar Didilli Amadou a matsayin sakatare janar na ma’aikatar tsaro, inda Salifou Modi ya zama Shugaban rundunar sojojin kasar sannan Birgediya Janar Seidou Bague ya zama Sabon Shugaban rundunar sojojin kasa ta kasar.

KU KARANTA KUMA: Hankula sun tashi a Edo yayinda mutum 2 suka mutu a rikici tsakanin manoma a makiyaya

Har ila yau An nada Birgediya Janar Sidikou Issa a matsayin babban sufeton sojojin kasa na kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng