Rarara Ya Dawo da Batun Sace Mahaifiyarsa, Ya Caccaki Atiku bayan Davido

Rarara Ya Dawo da Batun Sace Mahaifiyarsa, Ya Caccaki Atiku bayan Davido

  • Mawakin jam'iyyar APC, Dauda Kahutu Rarara ya buƙaci fitattun mutane su yi taka-tsantsan wajen yin tsokaci kan matsalar rashin tsaro a Najeriya
  • Ya ce yaɗa labarin sace mahaifiyarsa ya sa irinsu Atiku Abubakar shiga lamarin, wanda ya tsawaita zamanta a hannun wadanda suka sace ta
  • Dauda Rarara ya zargi Atiku Abubakar da yin kira a saki mahaifiyarsa a bainar jama’a wanda a cewarsa hakan bai taimaka ba wajen sakinta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Dauda Kahutu Rarara, ya buƙaci fitattun mutane su rika ja da baya a kan yadda suke yin magana game da matsalar rashin tsaro.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake sukar David Adeleke da aka fi sani da Davido, kan shigar da ya yi a bikin gasar cin kofin duniya a Amurka.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun gano abin da ke kullawa domin sauke manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Dauda Kahutu Rarara da Atiku Abubakar
Dauda Rarara a hagu da Atiku Abubakar a dama. Hoto: Dauda Kahutu Rarara|Paul O. Ibe
Source: Facebook

Dauda Rarara ya yi magana ne a wani bidiyo da ya yi kuma ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren Talata, 16 ga Yunin 2026.

Gargadin Dauda Rarara kan sha'anin tsaro

Rarara ya gargaɗi fitattun mutane kan abin da ya kira tallata ta’addanci, yana mai tuna sace mahaifiyarsa, wadda ya ce ta shafe ƙarin kwanaki a hannun masu garkuwa saboda yadda aka yaɗa labarin a kafafen sada zumunta.

Ya ce Idan ka wallafa irin labarun ana iya yada su zuwa ga miliyoyin mutane wanda hakan zai kawo cikas ga ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.

Rarara ya kara da cewa lamarin garkuwa da mutumin da ba kowa ya sani ba yana bazuwa a duniya idan aka yada shi a kafafen sadarwa.

Maganar Rarara kan Atiku Abubakar

Rarara ya yi magana kan abin da ya faru da shi na sace mahaifiyarsa, inda ya ce Atiku Abubakar ya yi amfani da kafafen yaɗa labarai wajen kira ga masu garkuwa su sake ta.

Kara karanta wannan

Rigimar Rarara da takwaransa ta munana, an shiga zagin juna a dandalin Twitter

Ya ce mutane da dama sun yi tunanin ya taimaka masa, amma a ra’ayinsa ya ce abin da Atiku Abubakar ya yi ba taimako ba ne.

Biyo bayan maganar Atiku, Rarara ya ce 'yan ta'addan sun kara tafiya da mahaifiyarsa cikin daji mai zurfin gaske maimakon su sake ta.

Dauda Kahutu Rarara
Mawaki Rarara sanye da rigar Bola Tinubu. Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Source: Facebook

Mawakin ya kara da cewa a sakamakon haka, wahalarta ta ƙara tsawo kafin daga bisani a ceto ta bayan kusan kwanaki 11.

Me Rarara ya so Atiku ya yi?

Rarara ya ce da gaske Atiku yana son taimakawa, da ya rubuta wa shugaban kasa, DSS, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda ko wasu hukumomin da abin ya shafa.

Daily Trust ta rahoto ya bayyana cewa Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasa ne kuma zai iya bayar da shawara mai kyau maimakon magana a intanet.

Mawakin Rarara ya soki Davido

A wani labarin, mun kawo muku cewa Dauda Kahutu Rarara ya caccaki mawakin Najeriya saboda ya yi korafi game da matsalar tsaro a Amurka.

Davido ya sanya riga dauke da sunayen daliban da aka sace a jihar Oyo yayin da ya yi wasa a wajen gasar cin kofin kwallon duniya na 2026.

A martanin da ya yi masa, Rarara ya nuna cewa hakan tamkar tona asirin Najeriya ne kasancewar Davido ya fadi matsalolin kasar a idon duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng