Mun shirya ma zaben da za a sake a Kano - INEC

Mun shirya ma zaben da za a sake a Kano - INEC

Kwamishinan zaben jihar Kano, Farfesa Riskua Shehu, ya bayyana a ranar Talata, 14 ga watan Janairu cewa hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zabe na gaskiya a zaben da za a sake a kananan hukumomi tara na jihar.

Ya ce wata kotun daukaka kara a Kaduna a zama mabanbanta da tayi, ta yi umurnin sake zabe a mazabun tarayya da na jiha wanda biyu suka kasance daga Kiru/Bebeji da Tudun Wada Doguwa tare da rumfunar zabe biyu a mazabar Kumbotso, rumfunar zabe hudu a sauran mazabun jiha na Bunkure, Maobi, Minjibir da kuma Rogo, wanda dukkanin jam’iyyun jihar za su shiga ciki.

A cewarsa, zaben da za a sake zai gudana ne a wuraren rijista 60 a fadin kananan hukumomin da lamarin ya shafa tare da masu zabe 41,400 da aka yiwa rijista a rumfuna 698, wuraren zabe 166, ina gaba daya ya zama wuraren zabe 864.

Ya ce ana saura kwanaki 11 za a gudanar da zaben, INEC za ta kasance da dukkanin kayayyaki a kananan hukumomin da lamarin ya shafa, kamar yadda aka fara kai kayayyakin yayinda hukumar ke jiran isowar kayayyakin zabe daga hedkwatar, cewa za a sanar da dukkanin jam’iyyun siyasa da zarar CBN ta karbe su.

Ya ci gaba da bayanin cewa “Za a aika sakon gayyata ga wakilan dukkanin jam’iyyun siyasa da za su kasance a zaben da za a sake da kuma hukumomin tsaro don ganin yadda za a yi rabon kayayyakin."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya nada tsohon Shugaban DSS a matsayin Shugaban NISS

Yayinda ya ke martani kan shirye-shiryen zaben, ya ce ma’aikatan zabe na wucin gadi 3,456 za a dauka inda ya ce babu dan bautar kasar da za a tura Bebeji domin aiki a matsayin ma’aikacin wucin gadi saboda shawarar tsaro.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel