Trump Ya Yi Maganar Ci Gaba da Kai Hari Iran duk da Cimma Yarjejeniya

Trump Ya Yi Maganar Ci Gaba da Kai Hari Iran duk da Cimma Yarjejeniya

  • Donald Trump ya ce yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Amurka da Iran ba ta ƙarshe ba ce, kuma tana iya fuskantar ƙarin bita
  • Shugaban na Amurka ya gargaɗi cewa ana iya komawa ga matakin yaki muddin Iran ta gaza cika abubuwan da ke cikin yarjejeniyar
  • Trump ya kuma yi barazanar kaddamar da sababbin hare-hare duk da rahotannin ƙoƙarin tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin Washington da Tehran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa rahoton yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) da aka cimma tsakanin Amurka da Iran ba yarjejeniya ce ta ƙarshe ba.

Shugaba Trump ya yi gargaɗin cewa za a iya komawa ga matakin yaki idan har bai gamsu da sharuɗɗan ba.

Trump ya ce zai iya komawa yaki da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Trump ya yi waɗannan kalaman ne a cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafin X ranar Laraba, 17 ga watan Yunin 2027 na kafar yada labarai ABC News.

Kara karanta wannan

"Suna farin ciki": Shugaba Trump ya fadi nasarar da ya samu a Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Shugaban kasar na Amurka ya bayyana cewa yarjejeniyar da aka sanar a farkon wannan makon tana kan ƙarƙashin bita.

Trump ya nuna shakku yarjejeniya da Iran

Kalamansa suna zuwa ne kwanaki kaɗan bayan rahotannin cewa Amurka da Iran sun cimma matsaya da nufin tsawaita tsagaita wuta, sake buɗe mashigar Hormuz, da kuma lafawar takaddama bayan share watanni ana rikici.

Sai dai, Trump ya ce takardar tana matsayin yarjejeniyar fahimtar juna ce kawai, ba kammalalliyar yarjejeniya ba.

“A’a, ba ta ƙarshe ba ce. Yarjejeniya ce ta fahimtar juna."

- Donald Trump

Shugaban kasar na Amurka ya ƙara da cewa sakamakon zai dogara ne akan ko ya amince da sharuɗɗan kuma ko Iran ta cika alƙawuranta.

Shugaban Amurka ya fitar da sabon gargaɗi

Shugaban na Amurka ya yi gargaɗin cewa lamarin zai iya komawa ga rikici idan har yarjejeniyar ba ta cika tsammaninsa ba, rahoton tashar Aljazeera ya tabbatar da hakam.

“Idan ban gamsu da ita ba, za mu koma kai hare-hare, da jefa masu bama-bamai."

- Shugaba Donald Trump

Kara karanta wannan

'Ni ne gatan Isra'ila': Trump ya fusata da lamarin Netanyahu a yaki da Iran

Trump ya yi gargadi kan yaki da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a Oval Office Hoto: Getty Images
Source: Getty Images
Ya kuma ce Amurka za ta iya sake farfado da hare-hare idan har Iran ta “yi ba daidai ba.” "Idan ban gamsu da ita ba, idan ba su yi hali na gari ba, za mu koma kan jefa bama-bamai a tsakiyar kawunansu."

- Shugaba Donald Trump

Shugaba Trump ya ce ayyukan Iran na baya a cikin “shekaru 47” su ne dalilin da zai sa Amurka ta ci gaba da matsawa ƙasar lamba.

Kasashen biyu dai sun cimma yarjejeniya domin kawo karshen yakin da aka fara a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026.

Trump ya ragargaji Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, yayi kakkausar suka ga mahukunta a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Shugaba Donald Trump ya siffanta shugabannin na Iran da “marasa daraja” saboda abin da ya kira bayanan ƙarya game da batun yarjejeniyar.

Donald Trump soki mahukunta a iran ne kan tseguntawa kafafen yada labarai bayanai dangane da yarjejeniyar da za a kulla.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng