Daga karshe: An saki jami’an kwastam 2 da aka sace a Katsina
Rahotanni sun kawo cewa wasu jami’an hukumar kwastam na Najeriya su biyu da aka yi garkuwa dasu sun kubuta daga hannun masu garkuwan bayan kwanaki hudu da sace su.
Kakakin Brigade 17, na rundunar sojin Najeriya da ke Katsina, Kyaftin Kayode Owolabi, ya bayyana hakan a wani jawabi a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu.
Kyaftin Owolabi ya ce: yan bindigan bayan kwada karfin rundunar sojin Najeriya sun saki jami’an kwastam su biyu a safiyar yau Lahadi, 12 ga watan Janairu, 2020.”
“Wasu yan shugabannin yan bindiga sun tura sakonni zuwa ga mukaddashin kwamandan sashi 8 na rundunar sojin Najeriya da ke jagorantar ayyuka a jihohin Katsina da Zamfara, inda suka nuna shirinsu na rungumar zaman lafiya ba tare da wani sharadi ba,” inji shi.
Ya ce: “Rununar soji za ta ci gaba da jajircewa domin tabbatar da aikin raba yan bindiga da makaminsu kafin su duba yiwuwar shiga yarjejeniyar zaman lafiya wanda gwamnatocin arewa maso yamma suka bayyana a baya.
KU KARANTA KUMA: Marasa zuwa Makaranta a Jihar Kano sun ragu da mutum kusan 1,000,000
A halin yanzu, rundunar Operation Sharan Daji na cigaba da abunda kwamandan ya kira da “Mop Up Ops” domin kakkabe dukkanin sansanonin yan bindiga don tabbatar da ganin sun saki mutanen da suka sace.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng