Osinbajo zai kaddamar da wasu manyan ayyuka a Kano

Osinbajo zai kaddamar da wasu manyan ayyuka a Kano

- Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar Najeriya zai kaddamar da wasu manyan hanyoyi a jihar Kano

- Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ce ta gudanar da ayyukan

- Zai kaddamar da hanyar karkashin layin dogo na Tijjani Hashim a Kofar Ruwa, gadar Aminu Dantata a Sabon Gari da sauran ayyukan da gwamnatin jihar Kano

Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, zai kaddamar da wasu manyan hanyoyi da Gwamna Abullahi Ganduje na jihar Kano ya yi aikinsu a ranar Litinin.

A lokacin ziyarar aikin na kwana daya a jihar, mataimakin Shugaban kasar zai assasa tushen gini na cibiyar kansa mallakar jiha ta farko a Najeriya.

Farfesa Osinbajo zai samu rakiyar Gwamna Ganduje da sauran manyan jami’an gwamnati a jihar.

Zai kaddamar da hanyar karkashin layin dogo na Tijjani Hashim a Kofar Ruwa, gadar Aminu Dantata a Sabon Gari da sauran ayyukan da gwamnatin jihar Kano karkashin Ganduje ta aiwatar.

Mataimakin Shugaban kasar zai kuma kafa tarihi idan ya assasa tushen cibiyar kansa ta Kano, wacce za ta zamo na farko mallakar jiha a kasar, da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Hankula sun tashi a Edo yayinda mutum 2 suka mutu a rikici tsakanin manoma a makiyaya

Ziyarar aikin zuwa Kano na zuwa ne kwana guda bayan Osinbajo ya jagoranci taron ranar rundunar tsaro na shekara-shekara a cibiyar Kirista, Abuja a ranar Asabar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel