An kama wani babban Fasto kan damfarar banki da sata

An kama wani babban Fasto kan damfarar banki da sata

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar Zimbabwe ta kama wani Shugaban cocin Manicaland Diocese Anglican Bishop Eric Ruwona kan rashawar $700 000.

Bishop Ruwona da abokansa a 2016, sun yi amfani da cocin Manicaland Diocese wajen aron $100 000 daga bankin Agribank, inda suka ikirarin cewa suna so su gina makarantar Saint Catherine’s Girls High School a Rusape da kuma siya wa faston mota.

An yi zargin cewa mai laifin ya yi amfani da fili mallakar cocin a matsayin jingina ba tare da sanin kwamitin cocin ba.

Sakamakon haka sai aka bayar da bashin inda mai laifin ya sanya kudin a aljihunsa.

A tuhuma na biyu, wanda ake zargin a wannan shekarar ya kuma neman bashin $350 000 duk daga wannan bankin.

KU KARANTA KUMA: Abin al’ajabi: Dalibi ya sharara ma malaminsa mari, ya caka masa wuka a kirji

Daga bisani sai faston da abokansa suka cire $250 000 daga asusun Agribank ba tare da sanin cocin ba.

Bishop Ruwona ya shafe dare shafe daren a ofishin yan sanda sannan ana sanya ran za a kais hi kotu yau.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng