Tashin Hankali: An Kashe Maza 2, An Sace Mutum 17 ciki har da Matan Aure a Sokoto
- ‘Yan bindiga sun kashe mutane biyu tare da sace wasu 17 a hare-haren Sabon Birni da Wurno, Sokoto, ciki har da mata da yara marayu
- Maharan sun kai farmaki gidaje a lokacin ruwan sama da daddare, suna fasa kofofi, inda suka kashe mutum ɗaya a Sabon Birni da wani a Wurno
- Mazauna sun ce rashin isowar jami’an tsaro cikin lokaci ya sa suka koma yin sintiri da kansu saboda yawaitar hare-haren a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Sokoto – Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun kai munanan hare-hare a ƙananan hukumomin Sabon Birni da Wurno a jihar Sokoto.
A yayin wadannan hare-hare, 'yan ta'addar sun kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu 17, ciki har da matan aure da yara ƙanana.

Source: Original
Harin 'yan bindiga a Sabon Birni
Wani mazaunin ƙauyen Tarah a Sabon Birni, ya ce 'yan bindigan sun kai hari kauyensu da daren ranar Talata zuwa safiyar Laraba, lokacin da ake ruwan sama, in ji rahoton Daily Trust.
Mutumin ya ce ‘yan bindigar sun isa ƙauyen da ƙafa da misalin ƙarfe 10:00 na dare, inda suka fara kai hari gida-gida suna fasa kofofi domin neman mutane.
Ya ce mazauna ƙauyen sun yi ƙoƙarin tunkarar maharan, amma suka fi su ƙarfi saboda makamai da suka zo da su.
A cewarsa, maharan sun shiga wani gida inda suka sace matan aure biyu da suka haɗa da Lami, matar Sani Tela, da Hajara, matar Lauwali Tarno, tare da yara biyar.
Ya ƙara da cewa cikin yaran da aka sace akwai marayu uku, yayin da sauran yara ke tsakanin shekaru biyar zuwa tara.
A yayin harin, maharan sun kashe wani mutum mai suna Nazifi Lauwali Kamtsa, sannan suka harbi wani mutumi a ƙafa.
Harin 'yan bindiga a Wurno ya yi muni
A wani harin daban, wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun farmaki ƙauyen Gidan Daji Alkammu a ƙaramar hukumar Wurno da misalin ƙarfe 1:00 na daren Laraba.
A nan ma sun kashe mutum ɗaya mai suna Hussaini tare da yin garkuwa da mutane 10, ciki har da mata shida da maza huɗu.
Wani mazaunin garin ya ce ruwan sama mai ƙarfi da aka yi a lokacin harin ya taimaka wa maharan wajen shigowa cikin sauƙi da kuma tserewa da waɗanda suka sace.

Source: Twitter
Martanin ‘yan sandan Sokoto
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce yana gudanar da bincike kan lamarin, inda ya bayyana cewa za su dawo da cikakken bayani daga baya.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, bai sake bayar da ƙarin bayani ba.
Wannan sabon hari na daga cikin jerin hare-haren da ke ƙara ta’azzara a jihar Sokoto, musamman a Sabon Birni, inda mazauna ke cewa matsalar tsaro na ƙara tabarbarewa a ‘yan makonnin nan.
'Yan bindiga sun hana noma a Sokoto
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun hana mazauna wasu yankunan Sokoto zuwa gonaki, sun ƙaƙaba musu sababbin haraji.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da korafi game da matsalolin tsaro da suka addabi sassan Najeriya da dama.
Mazauna jihar Sokoto sun bayyana cewa 'yan bindiga suna iya sake dawowa su bukaci karin kudi ko sun biya harajin a yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


