Cece-kuce a kan hawa jirgin shugaban kasa: Na kosa na kara samun wani aikin - Hanan Buhari

Cece-kuce a kan hawa jirgin shugaban kasa: Na kosa na kara samun wani aikin - Hanan Buhari

Hanan, daya daga cikin yaran Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta ce ta matsu ta sake samun wasu ayyukan karan kanta bayan na baya day a haifar da cece-kuce.

Hanan, wacce ta mallaki digiri mafi daraja a fannin daukar hoto daga jami’ar Ingila kwanan nan ta je jihar Bauchi domin aiwatar da aikin kanta cikin jirgin Shugaban kasa.

An tattaro cewa Rilwanu Adamu, sarkin Bauchi ne ya gayyace ta hawan daba, sannan yayinda ta je chan, ta dauki hotunan taron da kuma wasu wuraren jan hankali a jihar.

Yan Najeriya da dama sun yamusta gashin baki kan lamarin inda suka ce hakan zai kara yawan kudaden kula da jirgin a fadar Shugaban kasa. An ware naira biliyan 8.5 don kula da jirgin Shugaban kasar a kasafin kudin 2020.

Ana tsaka da wannan rigimar sai Aisha, uwargidar Shugaban kasa Buhari, ta wallafa biyon aikin Hanan a kafofin sadarwa ciki harda Twitter da Instagram.

KU KARANTA KUMA: Hankula sun tashi a Edo yayinda mutum 2 suka mutu a rikici tsakanin manoma a makiyaya

Da take martani ga wani mai amfani da shafin Instagram wanda ya yi sharhi a rubutun Aisha, Hanan ta ce ta matsu ta sake samun aiki na gaba.

Ta kuma yi godiya ga sauran yan Instagram da suka yi sharhi a aikinta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng