Wawan soja ne kadai zai yi tunanin juyin mulki – IBB

Wawan soja ne kadai zai yi tunanin juyin mulki – IBB

Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya) ya bayyana cewa zamanin juyin mulki ya dade da wucewa a Najeriya, cewa lallai wawan soja ne kadai zai yi irin wannan yunkuri.

Ya yi bayanin cewa anyi abubuwa da dama domin fitar da wannan tunanin daga kawunansu saboda ya daina samun karbuwa a duniya baki daya.

Janar Babangida wanda ya yi magana a shirin Channels Television ya nuna cewa mutanen zamaninsa za su yi duk abunda ya kamata don tabbatar da ganin cewa kasar ta ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki daya.

Tsohon shugaban kasar ya yi bayanin cewa idan har ana so kasar ta ci gaba toh zabar shugabanni na da muhimmanci.

Ya kara da cewa wajen zabar shugaban kasa, akwai abubuwa da dama da ya kamata a duba, ciki harda tunaninsa na hada kan kasar.

KU KARANTA KUMA: VAT da kudin lantarki za su tashi bayan kudirin tattali arziki ya zama doka

Ya ce mutanen zamaninsa na kallon hadin kan kasar a matsayin wani babi na imani sannan cewa basa shirin sake ganin wani yakin na basasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel