‘Ni ne Gatan Isra’ila’: Trump Ya Fusata da Lamarin Netanyahu a Yaki da Iran
- Donald Trump ya bayyana karfin tasirinsa a yakin da Isra’ila ke yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yankin Gabas ta Tsakiya
- Trump ya nuna matukar fushinsa kan Firayim ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yana zarginsa da dagula komai
- Shugaban na ƙasar Amurka ya ce yaƙin da ake yi da Hezbollah ya ɗauki lokaci mai tsawo, yana ba Isra’ila shawarwari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake bugun kirji game da yadda ya taimaka wa Isra'ila a yaki.
Trump ya yi iƙirarin cewa Isra’ila ba za ta wanzu ba da ba tare da taimakon Amurka da kuma jagorancinsa na kashin kai ba.

Source: Getty Images
Trump ya bayyana hakan ne yayin taron ƙasashen G7 da aka gudanar a Évian-les-Bains, kamar yadda shafin Israel Today ya ruwaito.
Tsagaita wuta ya jawo matsala tsakanin Isra'ila, Amurka
Rahotanni sun ce an samu rashin jituwa tsakanin Amurka da Isra’ila kan yadda za a tabbatar da tsagaita wuta a yankin Gabas ta Tsakiya.
Majiyar ta bayyana cewa Trump ya yi jawabin ne yayin da rikici ke ci gaba tsakanin Washington da Tel Aviv kan yaƙin Iran.
A ranar Lahadi, Amurka da Iran sun sanar da cewa sun cimma yarjejeniya domin kawo ƙarshen yaƙin yankin gaba ɗaya, ciki har da rikicin Lebanon da kuma sake buɗe mashigin Hormuz ga zirga-zirgar jiragen ruwa.
Sai dai Firayim ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana a ranar Litinin cewa dakarun ƙasarsa za su ci gaba da kasancewa a Lebanon duk da yarjejeniyar da aka cimma.
Netanyahu ya ce:
“Ina so in fayyace cewa za mu ci gaba da zama a yankunan muddin hakan ya zama dole domin kare ƙasarmu.”
Bayan sanarwar yarjejeniyar da Trump ya yi da Iran, Isra’ila ta kai hari ta sama a wani yanki na birnin Beirut, lamarin da ya ƙara tayar da hankali a yankin, cewar TheCable.

Source: Getty Images
Abin da ya fusata Trump game da Netanyahu
Trump ya ce ya fusata da Netanyahu saboda yadda yake rikita ƙoƙarin da ake yi na samar da zaman lafiya.
Shugaban Amurka, Trump ya ce babu buƙatar rusa manyan gine-ginen gidaje a duk lokacin da ake neman mutum guda, domin akwai fararen hula da dama da ba su da alaƙa da Hezbollah a irin waɗannan wurare.
Ya ƙara da cewa ya ba Isra’ila shawarar ta bar Syria ta magance matsalar Hezbollah, yana mai cewa a ganinsa kasar na gudanar da aikin fiye da yadda ake tsammani.
Trump ya ce:
“Idan da ba domin mu ba, ba don Amurka ba, da babu Isra’ila. Kuma ba tare da ni ba, da babu Isra’ila, domin babu wani shugaban ƙasa da ya yi abin da na yi. Ina da kyakkyawar alaƙa da Bibi, amma yanzu dole ne ya nuna dauki alhaki dangane da Lebanon.”.

Kara karanta wannan
Trump ya ballo ruwa, 'yan majalisa sun bude masa wuta kan shirin yarjejeniya da Iran
Sharudan Isra'ila kan yarjejeniya da Amurka
A wani labarin, an ji cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi ƙarin haske kan batun tattaunawa da Amurka da ake magana a yau Lahadi 14 ga watan Yunin 2026.
Duk da ikirarin Donald Trump cewa za a rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu, Tehran ta ce har yanzu ba ta yanke hukunci na karshe ba.
Har yanzu ana takun saka kan makomar shirin nukiliyar Iran da mashigin Hormuz, yayin da hare-haren Lebanon suka sake tayar da rikici.
Asali: Legit.ng

