Yanzu Yanzu: APC ta dau zafi yayinda sabon rikici ya barke a jam’iyyar

Yanzu Yanzu: APC ta dau zafi yayinda sabon rikici ya barke a jam’iyyar

Rikicin da ke faruwa a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya dauki sabon salo mai cike da damuwa a ranar Talata, 14 ga watan Janairu, lokacin da mambobin kwamitin masu ruwa da tsaki suka yiwa yiwa Shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole tawaye a lokacin taronsu na farko.

Lamarin is ya fara ne a ranar Talata lokacin da daya daga cikin mambobin kwamitin masu ruwa da tsakin ya ce lallai bai kamata ya jagoranci taron jam’iyyar ba saboda jam’iyyar reshen jihar Edo ta dakatar dashi bisa ka’ida.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan fitowa daga taron, mataimakin Shugaban jam’iyyar na kasa (Arewa maso gabas), Mustapha Salihu, ya jingina dalilin rikice-rikicen kan tsayar da Waziri Bulama don cike matsayin babban sakataren jam’iyyar na kasa.

Ya yi barazanar jan shi zuwa gaban hukumar DSS, da sauran hukumomin tsaro idan ya ci gaba da jagorantar kowani zama ba tare da dage umurnin da ya dakatar dashi daga jam’iyyar ba.

KU KARANTA KUMA: Mun shirya ma zaben da za a sake a Kano - INEC

Ya daura laifin dukkanin matsalolin da ke addabar jam’iyyar mai mulki kan tsohon gwamnan na Edo, cewa yana jagorantar jam’iyyar ta hanyar ajiye sunan Shugaba Buhari don tabbatar da ganin cewa duk wani hukunci ya yi daidai da son zuciyarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng