An Shiga Tashin Hankali da 'Yan Bindiga Suka Hallaka Basarake a Plateau
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi aika-aika bayan sun kai wani harin kwanton bauna kan basarake a jihar Plateau
- Hatsabiban 'yan bindigan sun tare basaraken ne lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida, inda suka farmake shi
- Majiyoyi daga yankin da lamarin ya faru, sun bayyana cewa kisan da aka yi wa basaraken ya jefa mutane cikin jimami da takaici
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - Wasu 'yan bindiga sun kashe Dagacin Gwande da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos a Jihar Plateau, Saf Samuel Alaket.
'Yan bindigan sun kashe basaraken ne a wani harin kwanton bauna da aka kai masa a kan hanyar mazaɓar Sha da ke iyaka da garin Daffo.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce majiyoyi a yankin sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:30 na daren ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan
Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito
Yadda 'yan bindiga suka kashe basarake
'Yan bindigan sun farmake shi ne lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida bayan kammala harkoki a sananniyar kasuwar ranar Talata da ke Daffo.
An tattara bayanai cewa marigayi dagacin ya halarci taron majalisar sarakunan gargajiya a Bokkos tun da fari, kafin ya kama hanyarsa ta komawa Gwande.
A cewar mazauna yankin, maharan sun yi wa motar basaraken kwanton bauna ne a kusa da iyakar da ke tsakanin mazaɓar Sha da kuma garin Daffo.
Dagacin ya samu munanan raunuka
An bayyana cewa basaraken ya samu munanan raunuka a lokacin harin, kuma cikin gaggawa aka garzaya da shi zuwa wani asibiti mafi kusa domin ba shi kulawar gaggawa.
Sai dai, duk da ƙoƙarin da ma'aikatan lafiya suka yi na ceto rayuwarsa, daga bisani ya cika sakamakon raunukan da ya samu, shafin Plateau Journal ya kawo labarin a Facebook.
Mutane sun shiga jimami
Wani mazaunin garin, Aten Pukat, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana mutuwar basaraken a matsayin rashi mai takaici ga mutanen Gwande da daukacin yankin Bokkos baki ɗaya.
Pukat ya ce harin ya jefa majalisar sarakunan gargajiya ta Bokkos da mazauna yankin cikin makoki, ya lura cewa ana girmama dagacin sosai saboda rawar da yake takawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaban al'umma.
Ya ƙara da cewa saƙonni na ta'aziyya sun ci gaba da kwarara daga hukumomin sarakunan gargajiya, shugabannin al'umma, da masu juyayi biyo bayan wannan babban rashi mai ban takaici.

Source: Original
Ƙoƙarin tuntuɓar mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Plateau, SP Alfred Alabo, domin samun ƙarin bayani bai yi nasara ba.
'Yan bindiga sun farmaki cibiyar NIPSS
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a cibiyar bincike kan manufofi da tsare-tsare ta kasa (NIPSS) da ke jihar Plateau.
Mugayen 'yan bindigan sun kashe mutane uku, ciki har da wani ɗan sanda yayin harin da suka kai a cibiyar ta NIPSS da ke a Kuru kusa da Jos.
Wata majiya ta tabbatar da cewa jami'an tsaro sun fafata da maharan a wata zazzafar arangama domin hana su samun damar shiga cikin cibiyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
