Za a Samu Canjin Shugabanni a Afrika, Gwamnatin Equatorial Guinea Ta Yi Murabus

Za a Samu Canjin Shugabanni a Afrika, Gwamnatin Equatorial Guinea Ta Yi Murabus

  • Gwamnatin kasar Equatorial Guinea ta kasa sauke nauyin da aka dora mata, wanda hakan ya sanya mutanen da ke cikinta yin murabus
  • Firaminista da sauran mambobin majalisar zartarwar kasar sun yi murabus daga mukamamsu, wanda hakan zai ba da damar nada sabuwar gwamnati
  • Mataimakin shugaban kasar, Teodoro Nguema Obiang Mangue, ya bayyana cewa gwamnatin ta gaza aiwatar da abubuwan da aka bukaci ta yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Kasar Equatorial Guinea - Teodoro Nguema Obiang Mangue, mataimakin shugaban ƙasar Equatorial Guinea, ya sanar da murabus ɗin majalisar zartarwa ta ƙasar.

Mataimakin shugaban kasar ya ce gwamnatin ta yi murabus ne bayan ta gaza cimma manufofin ayyukan da aka sanya mata.

Firaministan Equatorial Guinea ya yi murabus
Teodoro Obiang na jagorantar taron jami'an gwamnati a Equatorial Guinea Hoto: @TedoroObiang17
Source: Twitter

Teodoro Nguema Obiang Mangue ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, 16 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

"Sabuwar kungiyar ta'addanci za ta fara aiki a Najeriya," An gargadi Bola Tinubu

Meyasa gwamnatin Equatorial Guinea ta yi murabus?

Mangue wanda kuma ɗa ne ga Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, ya ce Majalisar ministocin ta yi murabus ne bayan ta cimma “kusan kaso 10 kacal” na manufofinta.

“Ƙa'idar tana da sauƙi: dole ne nauyin da aka rataya wa mutum a aikin gwamnati ya zo da sakamako mai kyau."
“Ƙasa tana sanya manyan albarkatun ɗan adam, kayan aiki, da na kuɗi a ƙarƙashin ikon gwamnati domin magance buƙatun al'umma."
“Don haka matakin ayyukan da aka fuskanta a fili yake bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da tsammani da kuma alƙawuran da aka ɗauka.”

- Teodoro Obiang Nguema Mbasogo

Mangue bai fito fili ya bayyana takamaiman manufofin da aka sanya wa majalisar ba.

Shugaba Mbasogo yana kan mulki tun a shekarar 1979, wanda hakan ya sa ya zama shugaban ƙasar da ya fi kowa daɗewa a kan mulki a duniya.

Ya naɗa gwamnati mai barin gado, wadda aka ɗora wa alhakin daidaita harkokin gudanarwa, a shekarar 2024, tare da Manuel Osa Nsue Nsua a matsayin firaminista.

Kara karanta wannan

Hadimin gwamna ya yi murabus kan rashin samun albashi na tsawon shekara

Ministoci a Equatorial Guinea sun yi murabus
Wasu daga cikin jami'an gwamnatin Equatorial Guinea a wajen taro Hoto: @TedoroObiang17
Source: Twitter

Ba a gamsu da kamun ludayin gwamnatin ba

A cikin wata sanarwa, jam'iyyar Democratic Party of Equatorial Guinea (PDGE) mai mulki ta ce shugaban ƙasar bai gamsu da yadda gwamnati mai barin gado ta gudanar da ayyukanta ba.

Mbasogo ya ce gwamnatin ba ta aiwatar da manufofin bunkasa sassa daban-daban na tattalin arziki ba, musamman a fannin noma, wanda hakan zai rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje waɗanda za a iya samar da su a cikin gida.

Ana sa ran cewa za a naɗa sabuwar gwamnati nan ba da jimawa ba.

Bola Tinubu ya yi nadi a gwamnatinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi nadi a hukumar NDDC mai kula da yankin Neja Delta.

Tinubu ya miƙa sunan Dr. Zainab Marwa ga Majalisar dattawa domin tabbatar da ita a matsayin mamba a majalisar gudanarwa ta NDDC, mai wakiltar shiyyar Arewa maso Gabas.

An yi nadin ne nufin cike gurbin da aka samu sakamakon murabus ɗin tsohon mamban hukumar da ya gabata, Hon. Abdulrazak Namdas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng