Mambobin Boko Haram da Lakurawa Sun Shiga Hannun 'Yan Sanda a Kebbi
- Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta bayyana nasarorin da ta samu a kokarin da take yi wajen samar da tsaro da yaki da ta'addanci
- Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayyana cewa an samu nasarar cafke wasu mutane da ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram da Lakurawa ne
- Hakazalika, ya bayyana cewa an samu nasarar cafke masu ba da bayanai ga 'yan ta'adda da masu ba su kayan aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta samu gagarumar nasara ta fuskar tsaro, wadda ta haɗa da kama mutanen da ake zargi da ta'addanci, 'yan bindiga da masu ba 'yan ta'adda bayanai.
Jami'an 'yan sanda na rundunar sun kuma samu nasarar ceto wata mata da aka yi garkuwa da ita, a cikin ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da aikata laifuffuka a faɗin jihar.

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa kwamishinan 'yan sandan jihar, Umar Hadejia, ya bayyana hakan yayin da yake jawabi jawabi a wurin taron manema labarai a Birnin Kebbi.
'Yan sanda sun samu nasarori a Kebbi
Umar Hadejia ya ce rundunar ta samu waɗannan nasarori ne a cikin watan da ya gabata ta hanyar amfani da bayanan sirri da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, ƙungiyoyin sa-kai, da kuma haɗakar jami'an tsaro na fararen hula (CJTF).
Ɗaya daga cikin manyan samamen ya kai ga kama mutane uku da ake zargi da zama mambobin ƙungiyar Mamudawa/Boko Haram a kan hanyar Illo zuwa Lolo da ke Ƙaramar Hukumar Bagudo a ranar 5 ga watan Yuni, 2026.
Yadda aka cafke wadanda ake zargi
Waɗanda ake zargin, waɗanda aka bayyana sunayensu da Muhammadu Bandi, Aliyu Abubakar, da Muhammadu Abubakar, an ce an kama su ne lokacin da suke jigilar kayan abinci zuwa ga miyagu masu gudanar da ayyukan laifuffuka a yankin.
Kwamishinan ya ce binciken farko ya danganta waɗanda ake zargin da zirga-zirga a kewayen Illo a lokacin wani hari da ya yi sanadiyyar mutuwar jami'an hukumar kiyaye haɗurra ta kasa (FRSC) guda uku a ranar 4 ga watan Yunin 2026.
An cafke 'yan ta'addan Lakurawa
A wani samamen na daban a ranar 7 ga Yunin 2026, jami'an 'yan sanda sun kama mutane huɗu da ake zargi 'yan ta'addan Lakurawa ne a kan hanyar Ka’oje zuwa Bakin Ruwa a karamar hukumar Bagudo, jaridar The Sun ta kawo labarin.
Rundunar 'yan sandan ta kuma kama wani da ake zargi da kai wa 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa kayan aiki.

Source: Original
A cewar kwamishinan, an kama Murtala Sani na ƙauyen Zazzagawa da ke karamar hukumar Argungu a ranar 9 ga Yunin 2026 biyo bayan rahoton sirri da ke nuna cewa yana kai wa mambobin ƙungiyar ta'addancin kayan abinci da abubuwan sha.
An kuma zarge shi da jigilar wani da ake zargi mamban Lakurawa ne zuwa maboyar miyagu a lokuta da dama.
'Yan bindiga sun kashe basarake
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka wani basarake a jihar Plateau yayin wani hari.
'Yan bindigan sun kashe basaraken ne a wani harin kwanton bauna da aka kai masa a kan hanyar mazaɓar Sha da ke iyaka da garin Daffo.
A cewar majiyoyi maharan sun yi wa motar basaraken kwanton bauna ne a kusa da iyakar da ke tsakanin mazaɓar Sha da kuma garin Daffo.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


