Matasan Yobe sun hau dokin naki kan zabar Bulama a matsayin sakataren APC na kasa

Matasan Yobe sun hau dokin naki kan zabar Bulama a matsayin sakataren APC na kasa

Matasan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Yobe sun nuna rashin amincewa da billowar Waziri Bulama a matsayin babban sakataren jam’iyyar na kasa.

Kungiyar matasan ta kuma yi watsi da matsayar jam’iyyar na kacaccala matsayin don sanya Borno.

Kujerar babban sakataren jam’iyyar na kasa ya kasance babu kowa tun bayan barij Mai Mala Buni, wanda ya kasance Gwamnan Yobe sai jiya Talata inda Bulama ya zama magajinsa.

Shugaban kungiyar matasan, Mohammed Shehu Gadaka, ya fada ma manema labarai a Damaturu, cewa Yobe ba za ta samu wakilci ba a taron masu ruwa da tsaki idan har aka baiwa Borno matsayin babban sakatare na kasa.

Ya bayyana hukuncin jam’iyyar kan lamarin a matsayin “rashin adalci da ka iya kawo rabuwar kai a tsakanin jam’iyyar sannan muna kira ga a gyara lamarin kafin jam’iyyarmu ta fada cikin rikici.

KU KARANTA KUMA: An kama wani babban Fasto kan damfarar banki da sata

Ya bayyana cewa jam’iyyar APC a jihar ta rigada ta zabi wanda zai maye gurbin Mai Mala kamar yadda aka tsara a farko amma sun rasa dalilin chanja shawarar da aka yi daga baya.

A jiya Talata ne aka nada Waziri Bulama a matsayin sakataren jam’iyyar na kasa a tsaka da kin amincewa dashi harma daga mataimakin Shugaban jam’iyyar a yankin arewa maso gabas, Mustapha Salihu wanda ya zargi Oshiomhole da cusa ma yankinsa Waziri.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng